A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya.
Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara.
Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa za su wanzar da ambatonsa a cikin zukatan masu rayayyen lamiri da kuma wadanda suke yin kira da tabbatr da ‘yanci a duniya.
Shugaban kasar na Iran ta kitse sakon nashi da cewa; A madadin ni kaina da kuma al’ummar Iran ina yin jinjina ga mamacin wanda ya yi fafutuka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.
A yau Litinin ne dai Fadar Vatican ta sanar da rasuwar Papa Roma Farancis wanda shi ne dan asalin yankin Latin na farko da ya jagoranci majami’ar .
Fadar ta kuma sanar da zaman makoki na kwanaki 9, sannan kuma ta sanar da cewa nan da makwanni biyu zuwa uku za a fara shirye-shiryen zabar sabon Papa Roma.