Leadership News Hausa:
2025-11-02@21:33:37 GMT

Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea

Published: 26th, March 2025 GMT

Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea

Fadar Gidan Gwamnatin Amurka (WhiteHouse), ta ce Rasha da Ukraine sun amincewa Jiragen jigilar kayayyakin kasuwanci gudanar da zirga-zirga cikin aminci a tekun Black Sea ba tare da kai musu hare-haren soji ba. Amurka ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jami’an Amurka sun gana da wakilan kasashen biyu a Saudiyya a ranar Talata.

Dole Ne A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro Sin Na Ci Gaba Da Kasancewa Cibiyar Rarraba Hajojin Da Masana’antu Ke Sarrafawa Sai dai Rasha ta ce, dole ne a dage wasu takunkuman da aka sanya wa bankuna, kamfanonin inshora, da masu fitar da abinci, kafin yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta fara aiki. Sai dai, Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da “kwarara karya” game da sharuddan yarjejeniyar. Rahotanni sun ce shugaban Amurka Donald Trump na ganawa da jakadun Amurka a fadar White House kan lamarin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.

Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa

An ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.

Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.

Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.

“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.

Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Allah Ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai