Ramadan Iftar: Sarkin Kauru Ya Hori Al’umma Su Hada Kai Su Zauna Lafiya da Juna
Published: 16th, March 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Kauru dake Jihar Kaduna Alhaji Zakari Ya’u Usman ya bukaci samun hadin kai da aiki tare kana da hakuri da juna tare da ɗaukar banbance banbance dake tsakanin al’umma a matsayin wata baiwa.
Alhaji Zakari Ya’u II yayi wannan horonne lokacin da aka taru a fadarsa dake Kauru domin shan ruwan azumin Ramadan.
Mai martaban ya bayyanawa wadanda suka taru domin wannan aikin lada na shekara shekara cewa, akwai bukatar yafiya da ‘yan uwantaka a wannan lokaci na Ramadan tare da godiya ga Allah da ya sake nuna mana wannan watan mai albarka.
Alhaji Zakaria Ya’u Usman yace akwai bukatar sadaukarwa da mika wuya ga Allah da kankantar da kai tare da fahimtar cewa wannan banbanci da ke tsakanin al’umma wata baiwa ce daga huwallazi tare da kira ga jama’a su nuna godiya ga Allah da wannan baiwar.
Yace Allah baya kuskure, saboda haka mu dauki wannan banbancin dake tsakanin mu a matsayi wata hanya ta aiki tare da nuna karfin mu na zama al’umma daya.
Sarkin Kauru ya godewa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani saboda samarda zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kaduna tare da gamsuwa da yunkurin karamar hukumar Kauru da jami’an tsaron wajen samar da kwanciyar hankali musamman kalubalen tsaron da wasu miyagun mutane suke haddasa wa a yankin.
Ganin yadda bukukuwan sallah ke karatowa, mai martaba ya hori talakawansa su kasance masu riko da kyawawan dabi’u da yafewa juna tare da tunatar da su cewa watan Ramadan ba wai ana magana akan azumi ne kadai ba, akwai bukatar ganin sa a ayukkan mu na yau da kullum.
Haka Kuma, sakataren masarautar Muhammad Sani Suleiman (Dan Buran Kauru) ya nanata kudurin masarautar na samarda zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar yankin.
Radio Nijeriya Kaduna ya bada labarin cewa an kammala wannan bikin shan ruwa na masarautar Kauru da gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban al’ummar yankin a daidai lokacin da ake shirin bukukuwan sallah.
Yusuf Zubairu Kauru
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ramadan Iftar Sarkin Kauru Zauna Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
Daga Abdullahi Shettima.
Ƙungiyar taimako mai zaman kanta mai suna Rays Heaven for Special Needs Children and Adults ta gudanar da taron wayar da kai a Kaduna domin ƙarfafa fahimtar muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ke shafar rukunin jama’a masu rauni.
Shugaban shirye-shiryen ƙungiyar, Sadiq Abdilatif, ya bayyana cewa wannan shiri mai taken Youth Resilience Project ana aiwatar da shi ne da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (European Union) tare da Global Youth Mobilization Fund.
Ya ce manufar shirin ita ce wayar da kai ga makarantun sakandare, al’ummomi, da sansanonin ’yan gudun hijira kan mahimmancin lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarfafa matasa su koyi magana idan suna fuskantar damuwa ko matsaloli, da kuma koyar da malamai da shugabannin al’umma hanyoyin taimaka musu.
Mr. Abdilatif ya bayyana cewa matasa da mutane masu buƙata ta musamman, ciki har da ’yan gudun hijira, na fama da ƙalubalen tunani da na tattalin arziki da ke rage musu ƙarfi wajen gudanar da rayuwa. Ya ce wannan shiri yana nufin gina ƙarfin gwiwa da samar da wakilai a cikin al’umma waɗanda za su ci gaba da yada wannan saƙo a yankunansu.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da shirin haɗa shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da ci gaba da wayar da kai a matakin ƙasa, yana mai cewa batun lafiyar kwakwalwa abin ne da ya shafi kowa.
Ɗaya daga cikin mahalarta shirin, Salma Hussaini, wadda ba ta da gani, ta yaba da yadda ƙungiyar ta haɗa masu buƙata ta musamman a cikin shirin. Ta ce ta amfana sosai wajen fahimtar yadda ƙarfin tunani da dogaro da kai ke taimakawa mutum ya shawo kan ƙalubalen da yake fuskanta duk da rashin lafiyar jiki.