Hamas Ta Yi Gargadin Bullar Yunwa A Gaza A Cikin Watan Ramadan
Published: 13th, March 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi akan cewa; Wata sabuwar yunwa za ta bulla a Gaza saboda yadda HKI take ci gaba da killace yankin da hana shigar da kayan agaji hatta a cikin watan Ramadan.
Kakakin kungiyar ta Hamas Abdullatif al-Qa’uni wanda ya fitar da wani bayani ya ce; Falasdinawa a yankin Gaza an killace su, makonni biyu a jere, kuma sojojin mamaya sun hana a shigar da kayan abinci,magunguna, da makamashi, wanda hakan yake a matsayin amfani da yunwa a matsayin makamin.
Qa’ani ya kara da cewa; Abinda ‘yan mamaya suke yi, shi ne jefa Falasdinawa cikin yunwa. Haka nan kuma ya ce; A nan gaba kadan kayakin da ake da su na bukatun yau da kullum za su kare a cikin Gaza, wanda hakan zai kara wahalar da mutanen yankin.
Kakakin kungiyar ta Hamas ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi matsin lamba akan HKI domin bude iyakoki da bayar da damar shigar da kayan agaji.
Tun a farkon wannann watan Maris da muke ciki ne HKI ‘yan mamayar su ka hana shigar da muhimman kayakin da ake bukata zuwa cikin yankin na Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Kori Ƙarar Neman Diyyar N1bn A Kan Buhari Da Emefiele Kan Sauya Fasalin Naira
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000.
Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa.
Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba.
Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba.
Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar.
Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya kori ƙarar, inda ya bayyana cewa mai ƙarar zai iya dawo da ita idan ya shirya yin shari’ar da gaske.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp