MDD, Ta Damu Da Matakin Isra’ila Na Hana Shigar Da Kayan Agaji Gaza
Published: 3rd, March 2025 GMT
Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya kira matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin dake shiga Gaza a matsayin abin damuwa.
Jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher, ya yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na katse taimakon da take baiwa Gaza, yana mai cewa abin takaici ne.
A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya tuna cewa “Dokar kasa da kasa ta bayyana karara cewa dole ne a bar agajin jin kai ya shiga zirin Gaza.”
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da dama da kwararru kan kare hakkin bil adama sun yi gargadin cewa wannan mataki ya zama keta dokokin kasa da kasa da kuma tauye hakkin bil’adama.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway (NRC) ta jaddada cewa dakatar da tallafin da Isra’ila ke yi gaba daya zai haifar da mummunan sakamako ga fararen hula fiye da miliyan biyu da tuni ke fuskantar yunwa.
“Taimakon jin kai ba gata ba ne, hakki ne,” in ji Angelita Caredda, darektan yankin NRC na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
A halin da ake ciki, kungiyar likitoci marar iyaka (MSF) ta yi kakkausar suka ga Isra’ila saboda amfani da agajin jin kai a matsayin makami.
“Bai kamata a yi amfani da taimakon jin kai a matsayin makamin yaki ba,” in ji kungiyar agaji ta likitoci ta kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa
Rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin, da rundunar ‘yan sandan kasar masu dauke da makamai, da dakarun sa-kai na cikin gida sun aike da dakaru domin shiga ayyukan ba da agajin gaggawa a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Sin.
A baya-bayan nan ne aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a gabashi, da arewaci, da arewa maso gabas na kasar Sin, lamarin da ya haddasa ambaliya da sauran ibtila’i na zaftarewar kasa da suka yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Rundunar ‘yan sanda masu dauke da makamai ta birnin Beijing ta aike da jami’ai da sojoji sama da 2,000 don taimaka wa ayyukan ba da agajin, inda aka kwashe sama da mazauna yankin da abin ya shafa 4,100 tare da kai akwatunan kayayyakin agaji fiye da 3,000 da tsakar ranar yau Talata. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp