LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya
Published: 28th, February 2025 GMT
Wadanda Suka Yi Nasara
Aliyu Usman Adam – Matsayi na daya
Aliyu Usman Adam, dan asalin Zariya ta Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a 2008. Bayan hidimar kasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014.
A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TB Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu.
Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu
Zainab Muhammad, wacce aka fi sani da “Indian Girl,” ‘yar asalin karamar hukumar Dala ce a Kano. Ta kammala firamare da sakandare a Kano, tare da burin ci gaba da karatun jami’a a nan gaba.
Zainab tana da kwazo a bangaren ilimin addinin Musulunci, kuma tana amfani da kafafen sada zumunta wajen ilmantarwa da fadakarwa. A halin yanzu tana da tarin masoya saboda rubuce-rubucenta masu kayatarwa da gina al’umma.
Mujaheed Nuhu Yusuf (Mujaheed Matashi) – Matsayi Na Uku
Mujaheed Nuhu Yusuf, wanda aka fi sani da Mujaheed Matashin marubuci ne a fagen wasan kwaikwayo kuma mawaki daga Kano. Ya wallafa littattafai biyu na wakoki, ciki har da Philosophy Mysterious Pen, wanda ya wallafa tare da marubuci Haiman Ra’ees.
Mujaheed shi ne shugaban kungiyar marubuta Ruhin Adabi, kuma yana wallafa rubuce-rubucensa a shirin Bakandamiya Hikaya da kuma shafinsa na Facebook.
Wannan gasa ta kara tabbatar da aniyar LEADERSHIP HAUSA na bunkasa hadaka da kirkirar rubutu a cikin al’ummar Hausawa. Jaridar na shirin ci gaba da shirya irin wadannan gasar domin karfafa sha’awar adabi da kuma karfafa dangantaka da masu karatu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gajerun Labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026
Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara amfani da cikakken tsarin amfani da Komfuta (CBT) ga dukkan jarabawar su nan da shekarar 2026. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin yayin ziyara da kuma duba yadda ake gudanar da gwaje-gwaje na CBT a cibiyoyin Bwari da kuma duba ɗakin gwajin jarrabawa JAMB a kwamfuta.
Alausa ya bayyana cewa, daga watan Mayu ko Yuni na 2026, duka ɓangarorin tambayoyin da aka saba na WAEC da NECO, na rubutu da na gwaje-gwaje, za su kasance a komfuta gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa wannan matakin na daga cikin manufar gwamnatin na magance matsalar satar jarabawa.
Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS WAEC Ta Kwace Lasisin Makarantu 574 Sakamakon Satar AmsaMinistan ya kuma sanar da cewa an kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Daraktan JAMB, Prof. Ishaq Oloyede, wanda zai duba tsarin jarabawar Nijeriya gaba ɗaya, inda aka ce sakamakon binciken zai fito nan da ƙarshen watan gobe. Alausa ya yaba da ingancin gudanar da jarabawar UTME ta 2025 da JAMB, wanda ya bayyana a matsayin “matsayi na duniya” kuma yana cika ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
A cikin jawabinsa, Oloyede ya bayyana cewa UTME ta 2025 tana ɗaya daga cikin mafi kyawun jarabawar da aka taɓa gudanarwa, inda ya kuma bayyana cewa duk wani zargin rashin dacewar cibiyoyin jarabawa yana buƙatar hujja mai ƙarfi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp