Aminiya:
2025-05-01@04:02:52 GMT

Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman

Published: 27th, February 2025 GMT

Wata Babbar Kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ake tuhuma da almundahana.

A ranar Alhamis, Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin sakin Farfesa Usman daga gidan gyaran hali na Kuje bayan an cika sharuɗan belinsa.

Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki

Hukumar EFCC ce, ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗe.

Ana zargin ya amince wajen sayen motoci a kan Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a matsayinsa na shugaban NHIS a 2016.

EFCC, ta kuma ce Farfesa Usman ya bai wa wani kamfani mai suna Lubekh Nigeria Limited kwangilar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta Naira miliyan 17.5 ta hannun ɗan uwansa, Khalifa Hassan Yusuf.

Duk da haka, Farfesa Yusuf ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Farfesa Usman

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa).

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu  gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman ayyuka da shirye-shirye tare da Bankin Duniya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Harkokin  kungiyar kasashen renon Ingila da Ci Gaban Birtaniya (FCDO), da Tarayyar Turai (EU), wanda hakan ya bata kwarewar da ta dace da sabon mukaminta.

Ya kara da cewa, Aisha Mujaddadi ta kasance a cikin kwamitoci da dama a matakin jiha da na tarayya, kuma ta taba zama memba a kwamitin gudanarwa na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna.

Sakataren Gwamnatin a jaddada cewa an yi nadin ne bisa cancanta, kwarewa da gaskiya, wanda ke nuna amincewar wannan gwamnati da kwarewar Aisha Mujaddadi.

Ya bayyana fatan cewa sabuwar Darakta Janar din za ta sauke nauyin  da aka dora a kanta tare da kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Jigawa.

Ya kara da cewa, nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin Darakta Janar na InvestJigawa ya fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
  • Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Kotu Ta Kori Ƙarar Neman Diyyar N1bn A Kan Buhari Da Emefiele Kan Sauya Fasalin Naira
  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA