Jagora : Kokarin Makiya Na Haifar Da Sabani Ya Ci Tura
Published: 17th, February 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura.
Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta da wani tasiri a kan wannan kasa da kuma al’ummarta.
Jagoran ya yi ishara da irin gagarumar fitowar al’ummar kasar a cikin jerin gwano da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci, wanda ya hambarar da azzalumar gwamnatin Pahlavi ta tsohuwar gwamnatin Amurka.
Ayatullah Khamenei ya sake ba da misali da irin dimbin abubuwan da suka faru a lokacin zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci a wannan shekara.
Bayan shekaru arba’in da cin nasarar juyin juya halin Musulunci, a daidai lokacin da ake tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci, dukkanin al’ummar kasar, sojoji, jami’ai, sun fito duk kuwa da irin matsalolin da ake fuskanta.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin Musulunci al ummar kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu.
Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.
Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu domin kara habaka tattalin arzikin ‘yan Najeriya da rage zaman kashe wando, da tayar da hankali musamman matasa a yankin.
Ya jaddada cewa dole ne gwamnatocin jihohi su tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da hukumominsu na jin dadin al’umma domin cimma burin shirye-shiryen.
A jawabinsa wajen taron, kwamishinan noma na jihar Sakkwato, Muhammad Tukur Alkali, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayo manyan Tan-tan na noma guda 250 da kayan aikin gona da darajarsu ta kai naira biliyan ashirin da biyu da miliyan dari daya (₦22.1bn), domin tabbatar da wadatar abinci.
A cewar Tukur Alkali, gwamnatin jihar ta hanyar shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma, ta samar da sama da ayyukan yi 2,700 a bangaren noma, abin da ke da tasiri mai girma wajen bunkasa noma mai dorewa da ci gaban ababen more rayuwa a karkara.
Daga Nasir Malali