Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe
Published: 30th, January 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar dabbobi.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdulkadir Tukur mai shekara 35 da Ibrahim Saidu mai shekara 20.
KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-RufaiAn same su da tumaki 28 da awaki 57, jimillar dabbobi 85 da ake zargin da sato su.
An kama su ne a ranar 25 ga watan Janairu, 2025, bayan da Dagacin Tulmi a Ƙaramar Hukumar Akko, Abubakar Umar, ya kai wa ‘yan sanda rahoto.
Wani mafarauci mai suna Yayaji Muhammad ne ya tare su a garin Tulmi, inda suka kasa bayar da cikakken bayani kan dabbobin da ke tare da su.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce jami’an ofishin Pindiga sun karɓi rahoton tare da fara bincike.
Ya ce waɗanda ake zargi sun amsa laifinsu, kuma har yanzu an mayar masu dabbobin guda 25 daga cikinsu.
Daga cikin mutanen da aka mayar wa dabbobinsu akwai Joseph Ahmadu da aka mayar wa da awaki shida, Bello Sintali da ya samu awaki huɗu, Godwin Iro da aka mayar wa da awaki 10, da Zaraya Jepter da aka dawowa da awaki biyar.
Dukkaninsu sun fito ne daga Jurara yankin Kashere da wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Akko da Billiri.
Haka kuma, wasu mutum huɗu da ake zargi da hannu a satar dabbobin sun tsere.
Waɗanda suka tsere sun haɗa da Rabe Saidu, Hamisu Saidu, Bode Saidu, da Wada Saidu, dukkaninsu daga ƙauyen Dawo a Ƙaramar Hukumar Kwami.
’Yan sanda na ci gaba da ƙoƙarin kamo su tare da ƙwato sauran dabbobin da aka sace.
DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar wa jama’a cewa suna ci gaba da bincike, kuma dabbobin da aka sace suna hannun ’yan sanda a matsayin shaida.
Ya ce dukkanin waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a kotu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, ya buƙaci jama’a su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi domin taimakawa wajen tabbatar da doka da oda a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda zargi da ake zargi
এছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.