Aminiya:
2025-09-18@00:44:36 GMT

Trump ya tiso ƙeyar rukunin farko na ’yan Najeriya daga Amurka

Published: 11th, September 2025 GMT

Rukunin farko na ’yan Najeriya da aka tsara korar su daga Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump sun bar kasar.

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a daren Laraba.

“Rukunin mutane 14 da aka kora daga Amurka, ciki har da ’yan Najeriya da wani dan kasar Gambiya, sun iso Ghana, kuma gwamnati ta taimaka wajen mayar da su kasashensu,” in ji Mahama a wani taron manema labarai.

Budurwa ta mutu a ɗakin saurayin da ke shirin auren ta a Abuja Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA

Ya ce Ghana ta riga ta shirya jigilar ’yan Najeriya zuwa kasarsu ta mota, yayin da ake ci gaba da taimaka wa dan Gambiya don shi ma ya koma kasar shi.

“Amurka ta tuntube mu don mu karbi ’yan kasashen waje da ba ’yan Ghana ba da za a fitar daga Amurka. Mun amince da cewa za mu karbi ’yan kasashen Yammacin Afirka,” in ji Mahama.

“Duk ’yan Yammacin Afirka ba sa bukatar takardar izinin shiga Ghana.”

Gwamnatin Trump dai a baya ta tuntubi kasashen Afirka da dama don su karbi ’yan kasashensu da aka kora daga Amurka a wani yunkuri na rage kwararar bakin haure.

Wasu daga cikin wadanda aka fitar dai ’yan kasashen Jamaica, Vietnam da Laos ne, inda kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke cewa hakan ya saba wa hakkinsu na asali.

Wasu kasashen sun nuna adawa da wannan tsarin na korar baki.

Najeriya, wadda ta sha bayyana matsayinta, ta ce ba za ta yarda da matsin lamba daga Amurka don karbar ’yan kasashen waje da ba ’yan Najeriya ba.

A watan Yuli, Amurka ta fitar da mutane biyar zuwa Eswatini da wasu takwas zuwa Sudan ta Kudu.

Rwanda ma ta karbi ’yan gudun hijira bakwai da aka kora daga Amurka a watan Agusta, bayan da kasashen biyu suka cimma yarjejeniya don karbar har mutane 250.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan Najeriya yan kasashen

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa