Gwamnatin Sakkwato ta ba jami’an tsaro tallafin motoci 14 da babura 150
Published: 5th, September 2025 GMT
Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar tallafin motoci 14 kirar Hilux da babura 150 ga dukkan jami’an tsaron jihar don karfafa aikin sintiri.
Tallafin kari ne a kan Hilux 170 da babura da gwamnatin ta bayar a baya.
Ba abin mamaki ba ne idan na fice daga NNPP – Abdulmumin Kofa ’Yan sandan Kaduna sun gayyaci El-Rufa’i kan zargin yunkurin tayar da zaune tsayeSakataren Gwamnatin jihar, Muhammad Bello Sifawa ne ya miƙa kayan a madadin Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu a wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka yi a gidan gwamnatin jiha a ranar Alhamis.
Bello Sifawa ya ce hukumomin tsaro ne suka roki a ba su ababen hawan a lokacin zaman majalisar tsaro ta jihar, shi kuma Gwamnan ya amince
Ya nuna bukatar da ake da ita ga jami’an tsaron kan su yi amfani da motocin da baburan ga abin da ake son a yi domin kare dukiya da rayukan jama’a.
Hakan a cewar Sakataren na cikin babban kudurin gwamnatin.
Da yake jawabi a madadin dukkan jami’an tsaron, kwamishinan ’Yan Sanda na jiha Ahmad Musa ya gode wa gwamnatin jiha kan amincewa da rokon nasu cikin lokaci
Kwamishinan ya kuma gode wa gwamnatin kan hadin kai da take bai wa jami’an tsaro, tare da bayar da tabbacin yin amfani da ababen hawan domin karfafa tsaro a jihar.
Ahmad ya ba da tabbacin jami’an tsaro za su ci gaba da aiki ba dare ba rana don tabbatar da zaman lafiya da taron rayuwa da dukiyar al’umma, za su taimaki gwamnati don samun nasara.
Kwamishina ya yi kira ga mutane su rika ba da bayani duk wani bakon abu da suka gani a yankunan su da ba su amince da shi ba, domin inganta tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Sakkwato jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025
Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025