Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gargadi Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Da Wasu Kasashe
Published: 1st, June 2025 GMT
Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka yi a baya, yana mai jaddada cewa Iran za ta dauki natakin da ya dace daidai ayyukan da sauran bangarori suka dauka.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a na kasa da kasa ya mayar da martani a jiya Lahadi kan rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi kan wasu batutuwan kariya da suka shafi Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wasu kafafen yada labarai sun wallafa wani bangare na cikakken rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, IAEA, Rafael Grossi, ya gabatar a jiya, wanda aka shirya gabatar da shi ga taron kwamitin gwamnonin dake tafe. Rahoton ya yi iƙirarin cewa yawan sinadarin Uranium da Iran ke da shi ya kai matakin da zai yi kusa da matakin da ake bukata wajen samar da makaman yaƙi kuma ya nuna rashin gamsuwarsa da Iran ke bayarwa duk da haɗin gwiwar da Iran ke yi da hukumar IAEA.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hukumar kula da makamashin nukiliya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Karin Maganar Sinawa: Koyar Da Su Ya Fi Bayar Da Kifi
Na san zuwa yanzu kowa zai amince cewa, kasar Sin ta bullo da sabuwar dabara ta abota da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da ya bambanta da ta masu son cin zali da neman iko. Koyar da fasahohin da za su taimakawa kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, zai kai su ga habaka ayyukansu da samar da sabbin dabarun ci gaba ta yadda za su habaka noma a cikin gida da sarrafa albarkatu har ma da shigar da su kasuwannin duniya. Wannan zai kai su ga samun wadata da ba su damar tsayawa da kafarsu. Tabbas wannan ya nuna cewa, kasar Sin aminiya ce ta kwarai mai son ganin dorewar ci gaban kasashe maimakon amfani domin mayar da su masu amshin shata, lamarin da zai kai ga cimma burin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp