Iran ta yi tir da kakkausar murya da harin Amurka kan tashar mai ta Yemen
Published: 19th, April 2025 GMT
Iran ta yi tir da Allah wadai da kakkausan lafazi da harin Amurka na baya baya nan kan tashar mai ta kasar Yemen, wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane tare da lalata dukiya mai yawa.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya kira harin da Amurka ta kai a matsayin keta kundin tsarin mulkin MDD da kuma dokokin kasa da kasa karara.
Misata Baghai ya ce : “Hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen, a matsayin cikakken goyon bayanta ga mamaya da kuma kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a yankunan Falasdinawa, ya sanya Amurka ta zama mai hannu dumu-dumu a kan laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Falastinu da kuma yankin.”
Akalla mutane 80 ne suka rasa rayukansu tare da jikkata wasu 150 a harin da Amurka ta kai kan tashar jiragen ruwan ta Ras Issa a Yemen.
Wannan dai shi ne hari mafi muni tun bayan fara farmakin na Amurka a Yemen yau sama da watanni 15.
Sojojin Amurka sun sanar da cewa sun kai hari tare da lalata tashar jiragen ruwa na Ras Issa da ke lardin Hodeida a ranar Alhamis da nufin hana ‘yan Houthi kudaden shiga da suke amfani da su wajen daukar nauyin ayyukansu da kuma ta’addanci a yankin.
Saidai ‘yan Houtsis, sun ce ‘’Ras Issa “tashar ruwa ce ta farar hula inda jiragen ruwa da ke dauke da mai da dizal da iskar gas ke isa domin raba mai ga dukkan yankunan Yemen.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar.
EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan daga nan take samun kasuwa a kasashen duniya. Kuma yan kasuwa daga kasahe fiya da 100 ne suka shigo kasar don halattan kasuwar.
Esma’il Bakaee, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce ya na fatan a wannan kasuwar, kasashen Afirka da Iran za su amfani juna a harkokin kasuwancin da ake bunkasa a tsakaninsu.