Aminiya:
2025-04-30@19:24:59 GMT

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba

Published: 6th, April 2025 GMT

Dakarun Soji  Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai.

Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa.

Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani

A cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa.

Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske.

Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle, inda suka tarwatsa sansanonin wasu ƙarin ’yan bindiga a baya-bayan nan.

Rundunar ta ce tana ci gaba da aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a faɗin Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Maɓoya Najeriya Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno

Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar.

Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.”

Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita 11 daga garin Rann, da misalin karfe 11 na safe a ranar Litinin.

Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya

Ta ƙara da cewa an kai wasu da suka jikkata asibitin Rann domin kula da su.

Babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren sojoji ko ’yan sanda game da faruwar lamarin.

Sai dai kuma, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Kenneth Daso, bai yiwu ba saboda layin wayarsa ba ya shiga.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
  • ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47
  • Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
  • Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno
  • Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
  • Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji kuskure ne — Janar Chibuisi