Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
Published: 2nd, April 2025 GMT
Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa.
Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi.
HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — JamusMasu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace.
Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi.
Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ruwa a Bayelsa, Kwamared Ogoniba Ipigansi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa har yanzu ba a samo mutum 13 ba.
Ya ƙara da cewa matsalar rashin ingantaccen yanayin sadarwa a yankin na hana aikin ceto tafiya yadda ya kamata.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba tukuna, amma sun fara bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bayelsa Hatsarin Jirgin Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Yemen na cewa katafaren jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki malakar klasarAmurka wato USS Harry Truman zai fice daga tekun red sea da nan kusa saboda makaman kasar Yemen da suka fada mata.
Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta nakalto wani jami’in ma’aikatar tsaron kasar wanda baya son a bayyana sunansa yana cewa, saboda yawan hare haren da sojojin Yemen suka kaiwa jirgin, wadanda suka hada da amfani da makamai masu linzami samfurin Crusse da kuma Balistic, har ila yau da jiragen yaki masu kunan bakin waken da suka fada a kansa. A yanzun ya zama dole jirgin ya fice daga tekun.
Tun cikin watan Maris da ya gabata ne gwamnatin shugaba Trump ta fara kaiwa kasar yemen hare-hare da jiragen sama wadanda suke tashi daga sansanin jiragen yaki da ke kan wannan jirgin. Saboda tilastawa kasar Yemen dakatar da kai hare-hare a kan HKI, don ta kawo karshen tallafawa Falasdinawa a Gaza.
Amma ya zuwa yanzu hare-haren na Amurka sun kasa kaiwa ga bukata, majiyar gwamnatin kasar ta yemen ta ce hare-haren Amurka a kasar ba zasu sa ta dakatar da tallafawa Falasdinawa, da kuma hanata kai hare hare kan jiragen kasuwanci na HKI masu wucewa ta tekun red sea ba.
A wani labarin kuma hare haren na sojojin yemen sun sa wani jiegin yakin Amurka samfurin F-18 ya fada cikin ruwa a tekun na Red Sea a kokarin kaucewa makaman sojojin Yemen.