Aminiya:
2025-09-18@01:00:24 GMT

Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a Faransa

Published: 2nd, April 2025 GMT

A wannan Larabar Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tafi ziyarar aiki ta makonni biyu a ƙasar Faransa.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai yi bitar ƙwazo da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faransa

এছাড়াও পড়ুন:

Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona.

Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar.

Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro

An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka gyara, amma sai mahukuntan Ƙungiyar suka yanke shawarar yin wasan a filin Johan Cruyff mai ƙarfin ɗaukar ‘yan kallo 6,000 kacal, wanda mafi yawan lokuta Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta mata Barcelona ke amfani da shi.

A gaba kuma, Barcelona za ta bakunci Newcastle United a filin wasa na St James’ Park a zagayen farko na gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) a ranar 18 ga Satumba. A gefe guda, Valencia za ta karɓi baƙuncin Atletico Bilbao a wasan mako na biyar na La Liga a ranar 20 ga Satumba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
  • Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya