Aminiya:
2025-04-30@19:24:58 GMT

Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdulahi Usman, ya rasu

Published: 26th, March 2025 GMT

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya.

Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago

Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

“SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba.

“Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi.

Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa da duk wanda ya san shi.

Sashen hulɗa da jama’a na ’yan sanda ya miƙa ta’aziyya ga iyalansa da kuma ‘yan uwansa, tare da yin addu’ar Allah Ya masa rahama.

Za a ci gaba da tunawa da Usman saboda sadaukarwar a aikinsa da ƙoƙarinsa na kyautata hulɗa tsakanin ’yan sanda da al’umma a Jihar Taraba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jinya Kakakin Yan Sanda Rashin lafiya rasuwa Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu zai ziyarci Katsina

Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai ziyarci Jihar Katsina.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Zango, ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce shugaban zai kai ziyarar ce, domin ƙaddamarwa da kuma rangadin wasu ayyukan da Gwamna Umar Dikko Radda ya aiwatar a jihar.

Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja

Karin bayani na tafe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Tinubu zai ziyarci Katsina
  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
  • Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
  • Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasu
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka Game Da Batun Haraji
  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran