Iran da Masar sun tattauna kan rikicin da Isra’ila ta jefa yankin gabas ta tsakiya
Published: 24th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tare da hana kai agajin jin kai a yankin a matsayin keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu.
Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin baki daya.
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta kasa cimma manufofinta da ta ayyana kan yakin, duk da kashe Falasdinawa 50,000 galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu fiye da 113,213.
Gwamnatin mamaya ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da shirin tsagaita wuta da kungiyar gwagwarmayar Hamas a Gaza, wadda aka fara aiki da ita a ranar 19 ga watan Janairu.
Bayan shudewar watanni biyu da fara aiwatar da yarjejeniyar, Isra’ila ta sa kafa ta yi fatali da ita, kuma ta ci gaba da kaddamar da hare-haren kisan kiyashi a kan al’ummar Gaza
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar.
EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan daga nan take samun kasuwa a kasashen duniya. Kuma yan kasuwa daga kasahe fiya da 100 ne suka shigo kasar don halattan kasuwar.
Esma’il Bakaee, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce ya na fatan a wannan kasuwar, kasashen Afirka da Iran za su amfani juna a harkokin kasuwancin da ake bunkasa a tsakaninsu.