Kasar Sin ta mika rijiyoyin burtsatsai 66 ga wasu yankunan lardin Mashonaland na gabashin Zimbabwe, wadanda za su samar da ruwa mai tsafta ga mutane kimanin 16,500.

Rijiyoyin wadanda kamfanin gine-gine na Geo-Engineering na kasar Sin ya gina, wani bangare ne na aikin hakar rijiyoyin burtsatsai 300 ga larduna 4 na kasar Zimbabwe.

Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i

Yayin bikin mika rijiyoyin da aka yi jiya, ministan kula da kananan hukumomi da ayyukan more rayuwa na kasar Daniel Garwe, ya ce aikin alama ce ta hadin gwiwa da tausayi da goyon baya daga aminiyarsu a kowanne yanayi watau kasar Sin, wanda aka yi domin tabbatar da samar da ruwa mai tsafta ga kowa.

Shi kuwa jami’in kula da harkokin kasuwanci da tattalin arziki na ofishin jakadancin Sin a Zimbabwe Huang Minghai, cewa ya yi, aikin ya kara karfafa hadin gwiwar Sin da Zimbabawe da ya shafe gomman shekaru. Ya ce cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta gina rijiyoyin burtsatsai sama da 1,000 a fadin kasar ta Zimbabwe, wadanda mutane kusan 400,000 ke ci gajiyarsu. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Kwara Ta Kwashe Mabarata Daga Titunan Jihar Su 94
  • Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa
  • Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
  • An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
  •  Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
  • Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
  • Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa
  • Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar