Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (2)
Published: 8th, March 2025 GMT
3.Mai dauriya / hakuri
Hakuri yana da matukar kyau ace kana da shi a matsayinka na Malami ka kuma nunawa dalibai domin su ta shi da shi, wadanda kamar yadda aka yi bayani cikin maganar dabarun koyarwa,suna iya daukarka, a matsayin wanda za su rika yin koyi da kai saboda su koyi halinka na hakuri.Matukar akwai hakuri za a samu saukin yin aiki tare da kowadanne matsaloli ko fadi tashin da dalibi yake yi,wanda hakan na iya zama masa babban wani tarnaki wanda zai wuyar gano bakin zaren,ko kuma abin ya zama tamkar tafiyar Kura.
4. A rika yin abubuwan jawo ankali
Dalibai suna fara koyo ne tun lokacin da suke ‘yan yara hakan kuma ne ya basu damar fadawa Malamai cewar su gaji da yadda kai Malami/ko Malamai suke koya ma su.Matukar kana son ka yi dalilin yadda ajin na ka zai zama abin burgewa,don haka idan ka gano yadda lamarin yake,sai ka yi amfani da damar wajen kawo masu misalan ra’ayoyin da za su jawo hankalinsu,har abin ya shiga zuciyarsu da kuma maida hankalinsu kan abinda ake koya masu!
5.Rika saurare sosai
Yin saurare hakan na da amfani saboda gane matsalar da bada taimakon yadda za ayi maganin abin wato su matsaolin.Ka nemi a baka irin halin da ake ciki,bada kwarin gwiwa bil hakki da gaskiya, samar da hanyoyin da dalibai za su rika tuntubar ka a saukake,ka kuma tsaida hankalinka duk lokacin da kake saurare,ko wane lokaci ka yi kokarin gane manufa lokacin da ake yin magana,ka kuma lura dakyau yadda labarin zuciya yake lokacin d a kake magana ko ake yi maka.Yi kokarin sanin me yasa d a kuma dalilin da yasa za kayi hakan
6.Mai/ Masu son abinda suke koyawa
Masana ilimi ba wai kawai suna sha’awar aikin koyarwar bane bugu da kari ma suna da sha’awa ta daukar lokaci mai tsawo suna kasancewar su ta masu koyo,wanda irin haka yana nunawa a gwagwarmayar su ta masu koyarwa. Ci gaba da koyo da bunkasar kwarewar kwararru irin hakan yana matukar taimakawa ta yadda kwararru za su kasance koda yaushe suna cikin “shirin kota kwana”da kuma tunatar da Malamai da irin matsalolin duniya mai nuna cewa dalibansu na iya fuskanta,sai kuma samar da wata dama ta nuna damuwa da abubuwan da suke damun wasu.Kara gano lamurran dangane da muhimmancin daukar lokaci mai tsawo ana koyo,da kuma yadda dabarun hanyoyin koyo za su taimaka maku ku koyar ko kuma gane/gano sababbin abubuwan da suka shafi ilimi.
7.Su zama basu da nuna bambanci
Matsayinka na mai ilimi zaka kasance da alhakin koyarda dalibai masu bambancin fahimtar ita koyarwar.Idan za ka yi maganin nuna bambanci,da kuma yin adalci,akwai bukatar ka rika gwada bukatar dalibanka,ta hanyar da babu nuna wani fifiko,abinda yake bukatar kai ka ci gaba da yin bincike da kuma bada bayani kan yadda ka fahimci ko nazarci wasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana
A gun taron manema labarai na musamman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar a yau Talata, jami’ai masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, yayin da manufofi da matakai daban daban na fadada kashe kudi ke ci gaba da yin tasiri a bana, kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin baki daya, sun ci gaba da nuna yanayin bunkasa bisa daidaito.
Jami’an sun kuma ce ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta inganta ayyuka na musamman don bunkasa kashe kudi, da gudanar da ayyuka a fannoni hudu, wato inganta yadda ake amfani da kayayyaki, da fadada amfani da hidimomi, da samar da gajiya daga sabbin kayayyaki, da kuma kirkirar sabbin yanayin cimma gajiya.
Ma’aikatar kasuwancin ta kuma bayyana cewa, za ta karfafa bincike kan manufofin da suka shafi amfani da fasahohin zamani, da kuma inganta ci gaba da amfani da kayayyakin dijital. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp