Gwamna Namadi Ya Karbi Lasisin Yin Kasuwanci Maras Shinge A Kan Iyakar Maigatari
Published: 6th, March 2025 GMT
Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa, kwamishinan kasuwanci, da masana’antu, Alhaji Aminu Kanta ne ya mika wa Gwamna Umar Namadi lasisin a ofishinsa.
Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati mai ci ta dukufa wajen gudanar da aikin karbar lasisin aikin daga NEPZA
A cewarsa, wannan ya nuna karara da kudurin gwamnati na bunkasa tattalin arziki, da inganta harkokin kasuwanci, da kuma sanya jihar Jigawa a matsayin babbar cibiyar zuba jari da bunkasa masana’antu.
Sakataren yada labaran ya yi nuni da cewa, kafa harkar cinikayya a kan iyakar Maigatari na da nufin jawo hankalin masu zuba jari na gida da waje, da inganta samar da ayyukan yi, da bunkasa harkokin kasuwanci, musamman a yankin arewacin Najeriya.
Ya ce, Gwamna Namadi ya nuna jin dadinsa ga kokarin hadin gwiwa da ya kai ga samun lasisin tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau don gudanar da kasuwanci yadda ya kamata.
Hamisu ya yi nuni da cewa, a karkashin gwamnatin Gwamna Umar Namadi, wannan yunkuri ya samu gagarumin ci gaba da nufin bunkasa tattalin arziki da habaka masana’antu a jihar.
Kwamishinan ya samu rakiyar Kodineta na shiyyar kasuwanci maras shinge ta Maigatari, Abdulaziz Usman Abubakar da mai kula da shiyyar Bello Abdullahi Nura.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta kaddamar da hare-hare kan yankuna da dama na Iran ciki har da Tehran
Isra’ila ta kaddamar da hare hare kan wasu gine-gine da cibiyoyi a sassa daban daban na Iran ciki har da Tehran babban birni a cikin daren jiya wayewar wannan safiya ta Juma’a.
Kafofin yada labarai na Iran sun ce akwai mata da yara da dama daga cikin wadanda suka yi shahada a hare-haren.
An kuma bayar da rahoton kai hari a wurare a Natanz, Khorramabad, da Khondab, da dai sauransu.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce harin da Isra’ila ta kai wa Iran zai kai tsawon kwanaki idab akwai bukatar hakan.
“Za a ci gaba da gudanar da wannan aiki na tsawon kwanaki kamar yadda ake tsara don kawar da wannan barazanar,” in ji Netanyahu a cikin wata sanarwa ta bidiyo.
Hare-haren da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka kai kan Tehran ya yi sanadiyar shahadar wasu fitattun masana kimiyyar nukiliya na Iran, Mohammad Mahdi Tehranchi da Fereydoon Abbasi, dama wasu fararen hula.
Tehranchi shi ne shugaban jami’ar Azad ta Musulunci ta Iran.
Fereydoon Abbasi ya kasance tsohon shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran.
An dakatar da zirga-zirgar jiragai a filin jirgin saman Imam Khumaini na Tehran.
Harin ya zo ne kwanaki biyu gabanin wani sabon zagaye na shawarwarin nukiliyar Iran da Amurka.