HausaTv:
2025-09-18@00:56:14 GMT

Iran : Jagora Ya Ba Da Tallafi Ga Fursunonin Mabukata

Published: 5th, March 2025 GMT

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya ba da gudummawar Riyal biliyan 40 ga wata kungiyar agaji da mai rajin ganin an sako fursunoni mabukata da aka samu da laifin aikata laifuffuka wandanda  ba na son rai.

A duk shekara, a cikin watan Ramadan, wannan kungiya mai zaman kanta ta kan kaddamar da kiraye-kirayen bayar da tallafi don tara kudade da biyan Diya, ta yadda za a saki fursunonin da ake yanke musu hukunci bisa aikata laifukan da ba da gangan ba.

Taron dai ya hada jami’ai da masu ba da agaji a Tehran babban birnin kasar da kuma garuruwa daban-daban na kasar duk shekara.

Diya wani hakki ne da ake biya ga wanda aka kashe ga magadansa, ko aka yi wa rauni ko kuma ba daidai ba.

Ramadan, wata na tara na kalandar Musulunci, lokaci ne mai matukar muhimmanci ga musulmi, wanda yana da muhimmanci a kula da marasa galihu da kuma taimakon mabukata.

Hakan ne sanya irin wannan lokacin Jagoran kan yi afuwa, ko sassauci ga wadanda ake tsare da bisa aikata wani laifi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

 

Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta