Hukumar bunƙasa ƙere-ƙere ta ƙasa (NASENI) ta bayyana cewa an kusa kammala aikin ƙera jirgin sama mai saukar ungulu na farko da aka yi a Nijeriya, kuma nan ba da jimawa ba za a fara gwajin tashinsa. Wannan ci gaba na daga cikin yunƙurin ƙasar wajen bunƙasa fasahar masana’antu da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Manajan Ayyuka na Cibiyar Bunƙasa Jiragen Sama ta NASENI, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa aikin yana kan hanya, inda ake amfani da dabaru na zamani don haɗa jirgin saman mai suna “Nigerian Chopper.” Ya ce hukumar ba wai tana ƙirƙiro wata sabuwar fasaha ba ne, sai dai tana inganta shirye-shiryen da aka fara tun farko, wanda ya haɗa da jirgin sama mai saukar ungulu da kuma jiragen sama marasa matuƙi (UAVs).

Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima… NASENI Ta Dukufa Kere-kere Domin Kawo Saukin Rayuwa A Nijeriya –Khalil

Injiniya Kareem ya bayyana cewa hukumar ta samo wasu sassa na jirgin sama daga ƙasashen da suka ci gaba a tsarin “Semi Knock Down” (SKD) da “Complete Knock Down” (CKD), tare da amfani da ilimin kimiyya da injiniyanci wajen haɗa su da inganta su. Ya jaddada cewa NASENI tana da himma wajen bunƙasa fasahar cikin gida domin rage dogaro da ƙasashen waje da kuma ƙarfafa masana’antu a ƙasar.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwajin tashin jirgin saman zai fara nan ba da daɗewa ba, yayin da ake kammala ƙarin cikakkun matakai na fasaha. Wannan aiki na daga cikin shirin gwamnati na ƙarfafa ƙere-ƙere da fasaha a Nijeriya don inganta harkokin sufurin sama na cikin gida.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.

Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa

An ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.

Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.

Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.

“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.

Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi