Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje
Published: 26th, February 2025 GMT
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa shugabancinsa ya gaji bashin Naira biliyan 8.9.
Ganduje ya bayyana haka ne a Abuja yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC.
Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC baA cewarsa, wannan bashi ya samo asali ne daga kuɗaɗen da aka kashe a shari’o’i kafin zaɓe, ƙalubalantar sakamakon zaɓe, da ƙarar da aka shigar da ’yan majalisu, gwamnoni, da na shugaban ƙasa.
“Shugabancin kwamitin zartaswa na ƙasa na yanzu ya gaji bashin Naira 8,987,874,663 da kuma tari shari’o’i daban-daban,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Farfesa Abdul Kareem Kana (SAN), na aiki don rage wannan bashi.
“Muna sake roƙon Kwamitin Zartarwa na Ƙasa da ya taimaka domin shawo kan matsalar,” in ji Ganduje.
Taron ya samu halartar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, gwamnonin jihohi da wasu manyan shugabannin jam’iyyar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.