NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri
Published: 24th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya.
Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya.
Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Jos ta Arewa da Bokkos da Shendam da Mangu da kuma Kenke.
Ko waɗanne irin matakai ya kamata al’umma su ɗauka don kauce wa kamuwa da wannan cuta?
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin AlbashiShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan matakan kariya daga cutar ƙyandar biri.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Annobar kyandar Biri cutar ƙyandar biri kariya ƙyandar biri matakan kariya matakan kariya daga cutar ƙyandar biri
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar.
Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar.
“Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.”
“Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da haƙuri yayin aikin Hajji. Da fatan za ku halarci dukkan tarukan bita da kai da aka shirya, domin muhimmanci su Alhazai” In ji shi.
Labbo, wanda ya sa ido a kan shirin rigakafin tare da bai wa wani mahajjaci daga Hadejia allurar farko, ya bayyana cewa aikin rigakafin zai ci gaba har zuwa lokacin tafiyar su zuwa ƙasa mai tsarki.
Haka kuma, Shugaban cibiyar lafiya a matakin farko, Dr. Bala Ismaila, ya bayyana muhimmancin allurar rigakafin da ake bayarwa, wanda ya haɗa da rigakafin cutar sankarau, cutar shan inna, da kuma cutar zazzabin cizon sauro (yellow fever).
Ya kuma yi bayani kan yiwuwar fuskantar rashin lafiya bayan rigakafin, inda ya shawarci mahajjata da su nemi kulawar likita cikin gaggawa idan suka fuskanci hakan ko wata matsala da ta wuce kima.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana gudanar da aikin rigakafin a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
Usman Muhammad Zaria