Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi, Yunusa Umar, ya jagoranci mambobi fiye da 7,500 zuwa jam’iyyar PDP. Cikin waɗanda suka sauya sheka har da Shugaban Matasa na APC a yankin, Yusuf Inuwa Bora, da Sakatare mai kula da jin daɗin mambobi, Isah Zakaria.

An karɓi waɗannan sabbin ‘yan jam’iyyar ne a hukumance a ranar Lahadi, inda Shugaban PDP na ƙaramar hukumar Dass, Hon.

Yusuf Sabo, da Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Mohammed Abubakar Jibo, suka tarɓe su. Umar ya bayyana cewa kyakkyawan shugabancin Gwamna Bala Mohammed ne ya sa suka bar APC.

Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu Da Aiki Tuƙuru

Ya jaddada cewa manufofi da shirye-shiryen gwamnan tun bayan hawansa mulki a 2019 sun amfanar da al’umma matuƙa. Ya ce suna da yaƙinin cewa PDP ce ke kula da walwalar jama’a, don haka ba su da dalilin ci gaba da zama a APC. Ya kuma tabbatar da cewa sabbin mambobin za su yi aiki tuƙuru don cigaban PDP a jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Jibo, ya bayyana wannan sauya sheƙar a matsayin babbar nasara ga PDP, yana mai cewa gwamnatin Bala Mohammed za ta ci gaba da ɗorewa kan hanyoyin cigaban jihar Bauchi. Ya kuma tabbatar wa sabbin mambobin cewa za su samu cikakkiyar damar zama ‘yan PDP ba tare da nuna bambanci ba.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: ƙaramar hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku

Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta.

A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu saboda lalacewar hanyar, abin da ke jawo gajiya da takaici ga fasinjoji da masu tuƙi.

An fara gina hanyar Gombe-Dukku-Darazo ne tun a shekarun 1980, aka gyara ta a farkon shekarun 2000. Sai dai daga baya aka yi sakaci da ita duk da kasancewarta hanyar da matafiya daga jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Bauchi da wasu ke bi.

“Gyaran motoci na cinye mana kuɗi”

Usman Abubakar, direba mai shekaru 45 da gogewar tuki na sama da shekaru 19, ya ce lalacewar hanyar na sa direbobi kashe kuɗi masu yawa wajen gyaran motoci.

Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu

“Gaskiya hanyar ta lalace matuƙa. A da tafiyar Dukku zuwa Gombe kan ɗauki mintuna 45, yanzu kuwa ko awa biyu ba ta isa ba. Rami ne a ko’ina, musamman daga Tongoyel zuwa Bojude da Bozonshulwa. Sau da dama idan ka fito da safe sai ka tarar da motoci sun tsaya cak a hanya. Shock absorber, gilashi da sauran sassan mota suna yawan lalacewa saboda ramukan hanyar,” in ji shi.

Ya ce a da ‘shock absorber’ na iya kaiwa shekara biyu kafin ya lalace, amma yanzu ko watanni uku bai yi ba sai ya karye. Hakazalika tsohon gilashi da ake siya ₦90,000 yanzu cikin sati biyu kawai sai ya fashe.

Usman ya kuma ce ya sha yin haɗura a hanyar cikin watanni biyu kacal, inda tayar motarsa ta fashe, ‘shock absorber’ ya karye, sannan kingpin ya lalace — duka sakamakon shiga ramuka.

Wani direba, Abubakar Hassan, ya ce lalacewar hanyar ta kai shi ga tunanin barin aikin tuƙi gaba ɗaya saboda asarar kuɗi.

“Idan ruwan sama ya sauka, tafiya sai ta koma tamkar azaba. Sau da dama motoci kan kwana a hanya saboda lalacewa,” in ji shi.

Fasinjoji sun bayyana ƙalubale

Kabiru Zubairu, ɗaya daga cikin fasinjojin da ke yawan amfani da hanyar, ya ce, “A da tafiyar kilomita 72 kan ɗauki mintuna 45 zuwa 60, yanzu ta koma awa biyu. Idan na taso Dukku da karfe 7:00 na safe, yanzu sai mu isa bayan 9:00. Wannan na jawo mana jinkiri sosai.”

Wani fasinja, Abubakar Aliyu, ya ce mutane da dama sun daina zuwa Gombe saboda halin hanyar. “Idan ka yi tafiya sai jikinka ya yi ciwo. Wasu matasa kan zuba yashi a cikin ramuka, amma ruwan sama yana wanke shi,” in ji shi.

Muhimmancin hanyar — Masana

Mai sharhi a harkokin jama’a, Sulaiman Sa’idu Liman, ya ce kusan kilomita 64 daga cikin 72 na hanyar Dukku zuwa Gombe sun lalace, kuma motoci yanzu ba sa iya wuce gudu na kilomita 20 a awa ɗaya.

“Hanyar na da muhimmanci ga tattalin arziki da walwalar al’umma. Ana jigilar kayan gona, kayayyakin lafiya da marasa lafiya ta wannan hanya zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) Gombe,” in ji shi.

Likita Aliyu Bashir kuwa ya ce lalacewar hanyar na haifar da matsaloli ga lafiyar jama’a, musamman ƙura da ke haddasa cutar asma, da kuma haɗarin haihuwa kafin lokaci ga mata masu juna biyu saboda girgizar mota.

Kungiyoyi da direbobi sun yi kira

Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dukku (DCF), Muhammad Bala Hashidu, ya yi kira da a gaggauta gyaran hanyar gaba ɗaya.

Shi ma shugaban Kungiyar Direbobi ta NURTW a Dukku, Abdulhamid Hassan, ya ce kusan kowace rana ana samun aƙalla motoci 10 da ke lalacewa a kan hanyar, abin da ya rage musu kuɗin shiga.

Gwamnati ta magantu

Mai magana da yawun gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da takwarorinta na Arewa maso Gabas domin samun tallafin Gwamnatin Tarayya wajen gyaran hanyar.

“Kwanan nan gwamnonin yankin sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu inda suka roƙi a gyara muhimman hanyoyi ciki har da wannan. Domin hanya ta tarayya ce, gwamnatocin jihohi ba su da ikon gyaran ta kai tsaye. Amma gwamnoni sun dage wajen ganin an gyara ta,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar