Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu (8)
Published: 22nd, February 2025 GMT
Ana matukar bukatar jami’an ilimi saboda kuwa sune suke da alhakin tabbatar dukkan tsare tsaren ilimi da manufofi ana amfani da su kamar yadda ya kamata.Suna aiki da Shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dalibai suna msaun nagartaccen ilimi.
Hakanan ma jami’an ilimi ma na bukatar su rika gabatar da horarwa ga Malamai da sauran ma’aikata kkan irin nau’oin dabarun na koyarwa da ba a dade da fara aiki da su ba.
Abubuwan da ake bukata daga jami’in ilimi
Shi da jami’in ilimi abubuwan da ke bukatar ya mallaka saboda irin gudunmawar da yake badawa a ko wace rana wajen daukar mataki.Babban abinda ake bukata kowace rana ana tabbatar da kowa da kowa yana samun irin ilimi mai nagarta da ya dace ya samu,ba ta re da la’akari da cewar shi wanene ba,ya ya yake,mai arziki ne ko kuma shi wani tantirin matalauci ne, ko kuma wane irin tafarkin addini yake bi.
Jami’an ilimi dole ne su tabbatar da bi dukkan shharuddan ilimi kamar yadda ya kamata, ba tare da wada wata maganar da bata kamata a yada ta ba, wajen huldarsu, dalibai, iyalai, da kuma abokan aiki.Bayan haka ma duk abinda da za su yi wanda ya shafi daukar mataki abu mafi dacewa shi ne su yi hakan ta byadda abin zai taimakawa mai koyo, sai kuma tafiyar da lamarin ilimi da gaskiya, ba tare da nuna wani bambanci ba, duba yadda lamrin ilimi yake, da kuma hanyar bada rahoto.
Jami’an ilimi bu da ake fison gani suna yi shi ne su guji nuna duk wani abinda ya sabawa gaskiya babu kuma wani bambanci ba, a duk wata hanya ta gudanar da aikinsu.
Hanyar da mutum zai bi domin ya zama jami’in ilimi
Idan har mutum yana bukatar zama jami’in ilimi ya kamata ya samu mallakar satifiket din digiri kan lamarin daya shafi ilimi ko kuma wani abu mai nasaba da shi, wannan ya hada da ya kasance yana da kwarewa kan lamarin daya shafi koyarwa ma’ana ko ya taba aikin koyarwa a cikin aji.
Wasu jami’an ilimin ana da bukatar su samu mallaki takardar shedar ko lasin da yake nuna cewar da akwai wani sashe ko bangare na ilimi da suka kware ko maida hankalinsu akai.
Hakanan ma idan mutum ya sani kan kwarai yadda zai iya tafiyar da mu’amalar sa da mutane, da kuma yadda yake ba lamarin muhimmanci sosai, da kuma irin wayo na yadda zai iya yin aiki da sauran abokan aikinsa subna daga cikin abubuwan da ake bukata ya mallaka domin ya samu nasara kan aikinsa. Idan dai an mallaki karatun da samun ilimin da ake bukata da kuma kwarewa, sai kuma dabaru,wadanda suke bukatar a dauke su domin su zama jami’an ilim suna iya fara neman aikin ta fannin da ba za su taba yin dana- sani ba.
Wannan shi ne rubutu na karshe kan ayyukan jami’an ilimi da muhimmancinsu, inda kuma muka fara da halayen kirki 14 da ake bukatar Malamin makarnta ya kasance da su.
Haleyen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Wurin Malamin makaranta (1)
Idan ka fara yin tunani kan ilimin ka wanda ka samu na can baya ba za ka taba mantawa da wani Mlamai ba wanda ya zame maka wanda za ka rika tunawa da shi domin yana baka ko ya baka kwarin gwiwa,kana kuma koyi da yadda yake tafiyar da rayuwar aikinsa ta Malamin makaranta.
Me yiyuwa shi ko Farfesa ne wanda ya sa ka canza sauya irin aikin da ka ke son yi, ko kuma Malaminne wanda yake koyawa yara kananan wanda saboda irin halin kirkin shi ne ya sa ma ka samu sauyi a rayuwar ta yaro karami.Kai wannan ma duk ba wani abu bane duk dai wani kokarain da ka yi a wani darasin da ake koya maka, akwai wasu halaye abubuwan da ake bukatar Malamin makaranta ya Kasane yana da sun a dabarun da za su taimaka ma sa wadanda za ayi magana kan su a cikin wannan maudu’in, wadannan kamar yadda aka tsara bayyana su ,sune wasu alamun halayen kirki da ake bukatar ace Malamin makaranta ya mallake su ko ace yana da su.
Sai a ci gaba da karantawa yayin da kuma za a hadu da wasu halayen kirki 14 da ake son Malamin makaranta ace yana da su kamar yadda masana ilimi suke bukatar haka shekara 2032 har ma gaba da hakan.
Kai abin ma ha rya zarce haka domin kuwa har ma da irin nau’in takardun ilimin da ake bukata kafin wani ya cancanci zama Malamin makaranta.Ko dai kana bukatar ka kara samun dabaru ne na salon koyarwa ,yadda za a koyar ya kuma zama da’iman ne ka mallake su, ko kuma halaye ne ya kamata ace kana da irinsu, koma dai me nene ya dace ka yi, wadannan shawarwarin ko nau’oin halayen su ne ake bukatar su zama maka kamar wata manuniya ta yadda za ka rika bunkasa ilimin ka, saboda ta hakan ne za ka samu damar inganta takardar da ke bada bayanai na ko wanene kai ta bangaren ilimin da ka mallaka ko kake da shi.
কীওয়ার্ড: Ayyuka Malamin makaranta kamar yadda ake bukatar
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku
A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Nijeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato.
Burin wadannan mata ta karu ne sakamakon yadda farin ciki nau’i uku ya lullube Malama Bela’u Sabo da iyalanta, bayan da ta haifi ’yan uku a garin Kaurar Yabo da ke Karamar Hukumar Yabo ta jihar.
Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargiA yayin da mai jego da angon karni da ’yan uwa suke tsaka da murna, wannan karuwar haihuwa ta kara jawo musu sha-tara ta arziki, inda matar gwamnan jihar, Hajiya Fatima Ahmad Aliyu, ta taso takanas zuwa kauyen ta domin yin barka.
Zuwa barkan wadannan ’yan uku ya faranta ran ba ma iyalan mai jegon ba, har ma da daukacin al’ummar garin Kaurar Yabo, domin kuwa, shi ne ziyarar farko da matar gwamnan Jihar Sakkwato ta taba kawo musu.
A yayin gaisuwar ne matar gwamnan ta gwangwaje Malama Bela’u da akwatuna uku cike da kayan fitar suna da tufafin jarirai da ragunan suna guda uku da buhuna 10 na hatsi da kuma tsabar kudi naira dubu dari biyar.
Ta kuma yi alkawarin bayar da irin wannan tallafi ga duk matar da ta da samu karuwar ’yan uku a jihar, lamarin da ya sa mata neman Allah Ya sa su a danshin wannan mai jego.
Haihuwar ’yan uku ta zo min da sauƙi — Mai jegoMalama Bela’u Sabo a tattaunawa da wakilinmu ta ce “a lokacin da na samu karuwar na yi tawakkali da Allah, kuma yaran da na samu Allah Ya yi masu albarka.”
Wakilinmu ya nemin jin yadda yanayin cikin da kuma haihuwar ’yan ukun ya kasance wa maji jegon, idan aka kwatanta da ’ya’ya takwas da ta haifa kafin su, inda ta shaida masa cewa, “akwai bambanci gaskiya don su ba su motsi, dayan ma ke dan motsi can ba a rasa ba.
“Na haife su babu wata matsala ko wahala, cikin sauki suka fito, kan haka ina fatan sake samun ’yan uku in Allah Ya ba ni don suna sanya farin ciki.
“Matar gwamna ta zo ta yi min barka, zuwan ya zo da muhimmanci, ta ba ni kudi dubu 500 da buhu 10 da akwati uku da kwalin sabulu da kwalin Klin da jirgin wanka.
“Yara ta kawo masu kala 42, ta ba ni kala 10 turame da leshi da sauran kayan shafawa, na gode Allah, Ya kuma saka da alheri,” in ji mai jego.
‘Na samu fiye da abin da na roka’Angon karni, Malam Sabo Kaurar Yabo, ya ce “A lokacin da na samu labarin na samu karuwar yaro uku a lokaci guda, sai na ji kamar an yi min kyautar Aljanna, farin ciki ya mamaye ni.
“Ina buri da rokon Allah Ya ba ni tagwaye sai na samu uku gaba daya, wannan ita ce haihuwa ta tara, yanzu ina da ’ya’ya 11 da mace guda.
“Har yanzu in zan sake samu ’yan uku zan yi maraba da su ganin yadda suke da dimbin alheri, don matar gwamna ta kawo min raguna da kimarsu ta kai naia miliyan biyu. Sun share min hawayena.
‘Zan so in sami ’yan uku’Ganin wannan irin kabakin arziki da kuma alkawarin mai tsoka da matar gwamnan ta sa wasu matan jihar kara kwadayin haihuwar ’yan uku.
Wata matar aure mai da daya da ke burin haihuwar ’yan uku, Suwaiba Sani ta shaida wa wakilimu cewa, “Abin akwai farin ciki! Matar gwamna ta kawo maka kaya don haihuwa, ka ga ’yan uku wasu mutane ne na musamman. Zan so in same su, matar gwamna ta hidimta min, na samu daukaka nima.”
A ranar Litinin da ta gabata wakilinmu ya samu labarin an sake samun karuwar ’yan uku a garin Addam da ke Karamar Hukumar Shagari.
Sai dai har zuwa kammala wanann rahoton, matar gwamna ba ta kai ga zuwa garin ba don cika alkawarin da ta dauka.
‘Kayan barka ba sa raino’Wasu matan jihar da wakilin namu ya zanta da su don jin ko za su so su haifi ’yan ukun, bayan wannan da matar gwamnan ta yi, sun nuna sabanin haka.
Maryam Ibrahim mai ’ya’ya huɗu ta ce ta sha wahalar rainoni tagwaye don haka ba ta son ’yan uku.
“Na samu ’yan biyu a haihuwa ta biyu, kula da su da wuya, ba na burin haihuwar ’yan uku gaskiya, don biyun na san yadda na sha wahalarsu, kayan barka ba su ne raino ba, ni kam hakan bai sauya ra’ayina.”
Sadiya Muhammad ta ce, “Ni ba ni da burin na haifi ’yan uku a rayuwata, amma idan Allah Ya ba ni zan yi murna, yanzu haihuwata biyu ta uku na kan hanya.”
“Alkawarin matar gwamna bai tura ni zuwa sanya raina ga abin da ban gani ba, kuma ita abin buki ne kawai za ta kawo, sauran kula da su har su girma ba ruwanta da shi fa.
“Amma da ta yi wani tsari na daukar nauyin karatun yara zuwa jami’a, da zai sa wasu kwadayin samun yaran don ganin za a rage masu wani nauyi ba harkar buki ba.”