Nijar: Taron Kasa Ya Bukaci Sojoji Su Yi Mulkin Rikon Kwarya na Shekara 5
Published: 20th, February 2025 GMT
Taron muhawara na kasar a Jamhuriyar Nijar, ya nemi sojoji su yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyar.
Haka zalika taron ya nemi a yi afuwa ga sojojin da sukayi juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Wasu shawarwarin kuma da mahalarta taron suka bukata ita ce, baiwa mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP, damar tsayawa takara a zabubuka masu zuwa, sannan a amince da islama a matsayin addini mai rinjaye a kasar.
Taron ya kuma bukaci rushe dukkan jam’iyun siyaya 172 a kasar.
A yayin rufe taron janar Tiani ya yi alkawarin biyan bukatun mahalarta taron.
A shekarar 2023 ne sojoji suka kwace mulkin Nijar, bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, bisa hujjar tabarɓarewar matsalar tsaro da rashin shugabanci na gari.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.
M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.
Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.
Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”
Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.
Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.
Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.