Buratai Ya Ɗauki Ɗamarar Ɗaga Likkafar Fasaha a Nijeriya
Published: 16th, February 2025 GMT
Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi ba.
Cibiyar ta Tukur Burutai ta haɗa hannu da da kasar Sin domin saukaka aikin tare da kuma inganta yanayin yadda za a gudanar da binciken.
Gidauniyar Buratai Ta Taya Giwa-Daramola Murnar Zama Shugaban Kungiyar Tseren Kwale-kwale Na Ondo Kingibe Ya Yaba Wa Tsare-tsaren Bunkasa Ilimi Ga Matasa Na BurataiBabban Manajan Daraktan cibiyar, Moses Ayom, ya bayyana nasarar da kasar Sin ta samu wajen gudanar da irin wannan bincike tare da ƙirƙirar ire-iren waɗannan na’urorin da ababen hawa.
Daga ciki akwai ababen hawa na motoci da suke amfani da lantarki kashi 80% tare da shafe nisan zagon tafiya me nisan Kilomita 500 zuwa 600.
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uSauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.
An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.
Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.