Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5
Published: 2nd, February 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Manchester City ta ci 5 da 1 a Gasar Firimiyar Ingila.
Ƙungiyoyin biyu sun ɓarje gumi da yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Emirates, a mako na 24 na gasar.
Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsaƊan wasan tsakiyar Arsenal, Martin Ordeegard ne ya fara jefa ƙwallo a minti na biyu da fara wasa.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Erling Haaland, ya warware ƙwallon da Arsenal ta jefa wa Manchester City, a minti na 55.
A minti ma 56 Thomas Partey ya ƙara jefa wa Arsenal ƙwallo ta biyu.
A minti ma 62 Lewis Skelly ya jefa ƙwallo ta uku, sai Kai Havertz ya jefa ƙwallo ta huɗu a minti na 76.
A minti na 93, ɗan wasan gaban Arsenal, Nwaneri ya ƙarƙare da ƙwallo ta biyar a raga.
Yanzu haka dai Liverpool ce ke jan ragamar teburin gasar da maki 56 daga wasanni 23, yayin da Arsenal ke biye mata da maki 50 daga wasanni 24.
Nottingham Forest tana mataki na uku, da maki 47 daga wasanni 24 s teburin gasar.
Ita kuwa Manchester City na mataki na huɗu a teburin gasar da maki 41 daga wasanni 24 da ta buga.
Manchester City na ci gaba da fuskantar matsaloli tun bayan da wasu manyan ’yan wasanta suka samu rauni, kuma a baya-bayan nan kyaftin ɗinta Kyle Walker ya bar ƙungiyar zuwa AC Milan da ke ƙasar Italiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arsenal Firimiya Ordeegard daga wasanni
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga
Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya.
Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai.
Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin TarayyaYa ce ƙorafin da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi na cewa an yi watsi da Arewa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da ayyukan ci gaba, wata dabara ce kawai don rage ƙimar shugabancin wanda ya fito daga Kudu.
Ya shawarci ’yan siyasar Arewa da su yi haƙuri, kamar yadda ɓangare Kudu ya yi lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya shugabanci ƙasar har na tsawon shekaru takwas.
“Shugaba Tinubu ɗan Najeriya ne kamar kowa. Ya cancanci yin shekaru takwas a kan mulki kamar yadda Buhari ya yi. Ka da mu lalata ƙasa saboda son zuciya,” in ji Onanuga.
Dangane da zargin cewa an fi bai wa ’yan Kudu muƙamai, Onanuga ya ce masu sukar Tinubu su kawo hujjoji da ƙididdiga maimakon su ci gaba da yin zargin da ba shi da tushe.
Ya ƙara da cewa babu wani yanki da ba shi da matsalar hanyoyi ko ayyukan da ba a kammala gama ba, amma ya ce gwamnatin yanzu na ƙoƙarin gyara abubuwan da ta gada.
“Kafin ku zargi gwamnati, sai ku binciki gaskiyar lamarin. Wannan duk siyasa ce kawai don a raina Shugaban Ƙasa,” in ji shi.
Onanuga, ya kuma kare matakin da Tinubu ke ɗauka wajen inganta tsaro.
Ya ce an samu ci gaba sosai, inda ya kafa misalin cewar dukkanin shugabannin tsaro daga yankin Arewa suka fito.
Ya ce yanzu yana iya yin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja cikin kwanciyar hankali, tafiyar da a da ta ke da hatsari sosai.