Kasar New Zealand Ta Gabatar Da Sabbin Sharuddan Barin Yahudawan Sahyoniya Shiga Kasar
Published: 28th, January 2025 GMT
Gwamnatin kasar News Zealand ta fitar da sabbin sharudda ga yahudawan HKI masu neman Visar Shiga kasar, daga ciki sai sun bada tarihin aikin sojen da suka yi a cikin kasarsu.
Takaita irin yahudawan da zasu shiga kasashen duniya bayana yakin Gaza dai, zai sanya wani tunani a zukatan yahudawan HKI musamman wadanda suka shiga yakin Gaza suka kuma yi wa Falasdinawa kissan kare dangi.
Kungiyoyi masu goyon bayan falasdinawa kimani 50 ne suka shigar da kara suka korafin a kissan kiyashe a Gaza wanda sojojin HKI suka yi a cikin watanni 15 da suka gabata a kotuna daban daban a duniya.
Gwamnatin kasar New Zealand dai tana tunanin hana duk wani soja daga cikin sojojin HKI wanda ya aikata kisan kiyashi a Gaza shiga kasarta. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar New Zealan ta haka akalla soja guda daga cikin sojojin HKI saboda kasancewa cikin sojojin da suka yi yaki a Gaza.
Jaridar Haaretz ta HKI ta bayyana cewa an sami irin wadannan korafe korafen a gaban kotuna a kasashen Afirka da Kudu, Sri Lanka, Belgium, Faransa, da kuma Brazil.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA