2025-06-13@17:25:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3938
«jami an kiwon lafiya»:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ware ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya domin tunawa da ranar da aka gudanar da zaɓen da ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci da adalci a tarihin ƙasar. Sai dai, bayan sama da shekaru 30 da gudanar da wannan zaɓe da kuma...
A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man. Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya. Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar...

Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu
Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka...

IPOB A Najeriya Ta Jawo Asarar Rayuka Kimani 700 Da Kuma Kudade Kimani Naira Triliyon N7.5 Tun Shekara ta 2021
Mutane kimani 776 ne suka rasa rayukansu sannan kudade kimani naira Triliyon N7.6 ne aka yi a sararsu a cikin shekaru 4 da suka gabata a yankin kudu maso gabacin Najeriya sanadiyyar zaman gida wanda kungiyar IPOB ta tilasta masu. Jaridar Premium time ta Najeriya ta bayyana cewa rahoton hukumar tsaro na SBM Intelligence ta...
Wani ɗan ƙasar Indiya, Harpal Singh, ya rasa ransa bayan katangar rumbun ajiya ta kamfanin ATCO da ke Zariya ta rushe a kansa ranar Talata. Mutumin dai daya ne daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke unguwar Cikaji a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa...
A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya...
A yau ne aka gudanar da taron ministoci masu daidaita ayyukan da aka amince, a gun taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, a birnin Changsha dake lardin Hunan na kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron, tare da karanta wasikar murnar bude bikin...
Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana shirin kafa dokar da za ta mayar da rantsar da shugaban kasar a kwaryar majalisar, maimakon yadda ake yi a dandalin taro na Eagle da ke tsakiyar birnin Abuja. DW ta ruwaito cewa ita dai Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 ta yi fice wajen dauko batutuwan da ke haifar da...
Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka ba tare da taɓarɓarewa nan da shekaru uku masu zuwa. Bankin ya yi hasashen haɓakar ma’aunin tattalin arzikin cikin gida, GDP da kashi 3.6 cikin 100 a shekarar 2025, sai kashi 3.7 a shekarar 2026 da kuma kashi 3.8 a shekarar 2027. Dalilin da...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta sha bamban da majalisun da ke goyon bayan masu goyon baya masu laifi misalin masu kisan gilla a Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada a yau Laraba cewa: Matsayin majalisar shawarar Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci...
Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar. LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana...
Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato. Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sake kunna ‘hanyar tayar da hankali’ zai gamu da martani mai ƙarfi na Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Fitar da kudiri kan Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta yi ba zai shafi kudurin al’ummar Iran...

He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince,...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasashen Afrika da suka zo kasar Sin domin halartar taron ministoci masu jagorantar aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin a taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika. Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tattauna...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara Jihar Neja domin jajanta wa mutanen Mokwa da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa. Zulum ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 300 domin taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa. Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar...
Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya. Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa...
Ana zargin wata mata mai suna Khadija kan zargin kashe ’yarta mai shekaru 11, Fadila, saboda Naira 100 da ta samu a yawon Sallah a unguwar Tukur Tukur da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, inda lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a unguwar har maƙwabta...
Cherki ya buga wasansa na farko a Lyon yana da shekara 16 a watan Oktoban 2019 kuma ya bar kungiyar inda ya ci kwallaye 29 sannan ya taimaka aka jefa 45 a wasanni 185 da ya bugawa kungiyar ta Faransa. Cherki ya wakilci kasar Faransa kuma ya lashe lambar azurfa a gasar Olympics da aka...
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a...
Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya shirya yin haɗaka da wasu ’yan siyasa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027. A wata hira da ya yi da BBC, Amaechi ya ce matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar ne...

Iran Ta Sami Nasara Akan Korea Ta Arewa Akarkashin Share Fagen Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Na Kwallon
Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Korea Ta Arewa da kwallaye uku masu kyau a wasan da aka yi a filin wasa na “Azadi” na Tehran. Kasashen biyu dai suna a karkashin; bangare na uku a Asiya saboda share fagen kai wa ga shiga gasar cin kofin kwallon...
Shugaban kasar ta Amurka wanda ya gabatar da jawabi a gaban sojojin kasar a sansanin ‘Fort Bragg’ dake Jahar North Carolina ya bayyana cewa; Jahar Los Angeles tana fuskantar mamaya daga makiya ‘yan kasashen waje.” Har ila yau shugaban na Amurka ya ce; Ba za mu bari a rika kai wa jami’an tsaron gwamnatin tarayya...
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓe shi kaɗai. “Ku bai wa Kudu tikitin, ku ga sakamako. Amma idan PDP ta ci gaba da tafiya a kan wannan kuskure, to, za ta fuskanci babbar matsala a 2027,” Yusuf ya bayyana. Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ba ɗa jam’iyyar...
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000. Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga...
Sai dai wasu daga cikin dillalan man fetur a Nijeriya na ganin ya kamata matatar ta riƙa sayar da lita ɗaya ƙasa da Naira 800, la’akari da cewa ana sayar mata da ɗanyen mai a kuɗin Naira maimakon Dala. Dangote dai ya nuna ƙwarin guiwar cewa kamfaninsa zai taka rawar gani wajen samar da isasshen...
Amma har zuwa yanzu, babu cikakken bayani daga Gwamnatin Tarayya. A watan Mayun 2025 ne Tinubu ya miƙa buƙatar samun amincewar majalisa domin karɓar rancen Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, ciki har da Dala biliyan biyar daga Aramco. Rahoton Reuters bai bayyana sunayen bankunan da za su taimaka ba, amma majiyoyi sun ce ɗaya...
A cewarsa, shuwagabancin Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yanke hukunci masu wahala amma masu amfani. Dangane da sauyin jam’iyyun siyasa da ke faruwa, Namadi ya ce yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC alama ce da ke nuna yadda jama’a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma burin da yake...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar...
Iran ta bada sanarwan cewa ta sharia matakan da zata dauka kan hukuma IAEA mau kula da makamashin nukliya ta duniya idan ta samar da kudurin yin allawadai ko kuma rashin bada ahadin kai ga hukumar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ik Baghae yana fadara...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin...
Mahara sun kone gidaje akalla 96 a yankin Gyenbwas na gundumar Langai da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato. Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun kuma kwashe musu kayan abinci da katifu da kuma shanu da sauran kayayyaki. Alhaji Yakubu Umar, wanda kuma shi ne Madugun Langai ne ya shaida wa...
Kasashen Sin da Kenya sun zurfafa hadin gwiwarsu a bangaren kiwon lafiya, inda kasar Sin ta bayar da guraben tallafin karatu 500 da kaddamar da shirye-shiryen musaya 20 a kwacce shekara. Wata sanarwa da aka fitar bayan taron da aka yi tsakanin jakadar Sin dake Kenya Guo Haiyan da babban sakataren ma’aikatar lafiya ta kasar...
Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alau da ya haifar da ambaliya a bara. Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam ɗin amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya...
Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alou da ya haifar da ambaliya a bara. Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam din amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya...
LEADERSHIP ta tuna cewa, gwamnatin jihar da jami’an tsaro sun fuskanci matsin lamba daga mazauna yankunan da lamarin ya shafa domin shawo kan lamarin. Fanwo, ya ba da tabbacin cewa, gwamnati ta yi shiru, amma tana samun nasara a yakin da take da masu aikata laifuka ta karkashin kasa, musamman masu garkuwa da mutane...
Da safiyar yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Koriya ta kudu Lee Jae-myung ta wayar tarho. Da farko, Xi Jinping ya sake taya Mista Lee murnar lashe babban zaben shugaban kasa. Sa’an nan, ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da Koriya ta Kudu su tsaya tsayin daka...

Kyakkyawar Hulda Tsakanin Sin Da Koriya Ta Kudu Na Da Muhimmanci Ga Zaman Lafiya Da Ci Gaban Yankinsu
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Korea ta Kudu da su daukaka dangantakarsu zuwa matsayi na gaba ta yadda al’ummominsu za su kara amfana da ita da kawo tabbaci ga duniya mai cike da rashin tabbas, yayin da yake taya Lee Jae-myung murnar lashe zaben shugabancin...
Nijeriya tana fuskantar tsaiko a tattaunawar da ake yi da kamfanin man fetur mafi girma a duniya mallakin Saudiya wato Aramco, dangane da shirin karɓar rancen Dala biliyan biyar. Wani rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya bayyana hakan da cewar Nijeriyar na neman rancen kuɗin ne wanda take shirin ƙulla yarjejeniyar biya da...
Gwamnan ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Neja kan mummunar barnar da ambaliyar ruwan ta yi, na salwantar da rayuka da barnata dukiya da dama. Gwamna Umar Bago na jihar Neja, ya yabawa takwaransa na Borno bisa wannan ziyarar da kuma bayar da gudunmawar, inda ya ce lokaci ya yi da za a...
Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jajanta wa al’ummar kasuwar katako ta bayan kara da ke Birnin Kebbi bisa ibtila’in gobara da ta auka musu. Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa. A saurari sauyin da...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa, a halin yanzu Jamhuriyar Musulunci za ta iya kai wa Isra’ila hari “daidai” inda ta ke so bayan samun bayanan sirri kan cibiyoyin nukiliyar gwamnatin Isra’ila. Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wata wasika mai zuwa ga ministan leken...
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Dr. Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa har yanzu cutar kyandar biri wato Mpox na kasancewa mai matukar hadari a faɗin duniya. Wannan sanarwa ta biyo bayan taro na hudu da kwamitin gaggawa na kiyaye dokokin harkar lafiya na duniya IHR ya gudanar a ranar 5 ga Yunin 2025, domin nazarin...
Masu bayar da agajin gaggawa sun isa wurin jim kadan bayan karfe 9 na safe, inda hargitsi da firgici ya da baibaye mazauna harabar makarantar. A cewar ‘yansandan yankin, dan bindigar ya shiga ajin karatun ne dauke da bindiga inda ya bude wuta kan mai uwa da wabi, sannan kuma ya harbe kansa. ...
A wani taron sauraron bayanai da aka gudanar a kwanan baya, ‘yar majalisar wakilan kasar Amurka Madeleine Dean ta yi wa ministan kasuwanci na kasar, Howard Lutnick tambayoyi game da yanayin ciniki da manufofin harajin kwastam na kasar, inda ta tono shirmen da ke cikin matakan haraji da Amurka ta dauka a kan kayayyakin da...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce nan ba da jimawa ba al’ummar Nijeriya za su ga gagarumin sauyi a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar. Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar mansa da ke yankin Lekki a Jihar Lagos....