Yadda jami’an tsaro suka kashe ’yan ta’adda a musayar wuta 50 a Neja
Published: 30th, August 2025 GMT
Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja.
Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar.
Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro.
Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a BauchiYa ruwaito shaidu na cewa ’yan ta’adda kimanin 300 ɗauke da makamai ne suka yi yunƙurin kutsawa ƙauyen a ranar Talata.
“Sun yi nufin kai hari ne a wani sansanin Hukumar Tsaro ta DSS, amma jami’an tsaron suka mayar da martani suka kashe kimanin 50 daga cikin ’yan bindigar wasu da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbi.
“Al’ummar mazaɓata sun tabbatar min cewa sun ga yadda ’yan ta’addar saboda tsabar girgiza, suka riƙa sassara gawarwakin abokansu suna sanyawa a cikin buhuna, suna tafiya da su a kan baburansu.”
A wani labari makamancin wannan kuma, ’yan bindiga sun kashe wani manomi tare da jikkata wasu a yankin Kundu da ke kusa da garin Zungeru a Ƙaramar Hukumar Rafi a ranar Alhamis.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan ta adda Garkuwa Ƙaramar Hukumar jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura.
Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki.
Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO.
Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin da muke ƙoƙarin biyan ragowar kuɗin wutar,” in ji sanarwar.
Ambaliya: An gano gawar ’yar shekara 3 da ruwa ya tafi da ita a Zariya Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makonTa bayyana cewa a yayin da take ƙoƙarin biyan bashin da kamfanin ke bin sa, yana da muhimmanci a fahimci cewa yanke wutar lantarki daga muhimmiyar cibiyar lafiya babbar barazana ce ga majinyata da danginsu.