Magauta sun sa NNPCL a gaba – Ojulari
Published: 29th, August 2025 GMT
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari ya ce mutanen da ba sa nufin Najeriya da alheri sun sa kamfanin a gaba saboda sabbin tsare-tsaren da yake kawowa na inganta fannin man fetur a kasar.
Ya bayyana hakan hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Manyan Ma’aikatan Bangare Man Fetur da Iskar Gas na Kasa (PENGASSAN) a hedkwatar kwamfanin da ke Abuja.
Ojulari ya ce duk da yake sun san za su iya fuskantar kalubalen, amma ba za su taba bayar da kai bori ya hau ba a yunkurinsu na inganta rayuwar ’yan Najeriya.
“An sa mu a gaba, amma ba za mu taba bayar da kai ga biyan bukatar dan lokaci ba, saboda hakan ba zai haifar wa da Najeriya da mai ido ba. Mun san ba yadda za a yi ka kawo canji ba tare da kalubale ba,” in ji Ojulari.
Shugaban kamfanin ya bukaci ’yan Najeriya su kara hakuri da sauye-sauyen, inda ya ce bayan wuya dadi na nan tafe ba da jimawa ba.
Tun da farko shugaban kungiyar ta PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce ma’aikatan na man fetur sun je hedkwatar kamfanin ne domin su gode masa kan irin gudunmawar da ya bayar a taron kungiyar na bana da aka yi kwanan nan a Abuja.
Ya kuma ce suna jinjina wa shugaban na NNPPCL saboda abin da ya kira gagarumar nasarar da ya samu ya zuwa yanzu a karkashin shugabancinsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ojulari
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.
Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.
Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.
“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.
Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.
Tinubu ya kuma yaba wa masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.
Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.
Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Daga Bello Wakili