Kasashen AES zasu kafa kotun hukunta manyan laifuka ta kungiyar
Published: 2nd, June 2025 GMT
Ministocin shari’a na Burkina Faso, Mali da Nijar sun amince da kafa kotun hukunta laif uka da kare hakkin bil’adama ta kungiyar tarayyar kasashen Sahel.
Haka kuma za a gina wani gidan yari mai cikakken tsaro a yankin, mai alaka da wannan kotun, domin karfafa hanyoyin yaki da ta’addanci da aikata laifuka a yankin.
Sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a birnin Bamako a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu.
Kotun hukunta manyan laifuka da kare hakkin bil’adama a yankin Sahel A cewar shafin labarai na APANews, za ta dauki nauyin “duba laifukan cin zarafin bil’adama, laifuffukan yaki, kisan kiyashi da ta’addanci, halatta kudaden haram da kuma cin zarafi mai tsanani na ‘yancin dan adam da sauran manyan laifuka masu alaka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.