Hukumar Kula Da Kasuwa: Adadin Kamfanoni Masu Zaman Kansu A Kasar Sin Ya Zarce Miliyan 57
Published: 21st, April 2025 GMT
Hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ya zarce miliyan 57 ya zuwa karshen watan Maris, wanda ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar baki daya. Kazalika, a rubu’i na farko, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu da aka kafa a kasar ya kai miliyan 1.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.