Farashin fetur ya ƙaru sakamakon hana Dangote mai a Naira
Published: 30th, March 2025 GMT
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa.
A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira.
Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin MusulmiWannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
Rahotanni sun nuna cewa farashin ya fi ƙaruwa a Arewa, yayin da Legas ke da mafi ƙarancin farashi.
Kamfanin MRS Oil & Gas na jigilar mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
Duk da haka, ba a bayyana takamaiman wajen da aka sayo sabon man fetur ba, amma yanzu ana sayar da shi a farashin da ya bambanta da na baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: farashi Ƙari Matatar Dangote
এছাড়াও পড়ুন:
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.
Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp