SDP: Ba Mu Yi Wa Kowa Alƙawarin Takarar Shugaban Ƙasa Ba
Published: 25th, March 2025 GMT
“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi.
“Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a”Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba.
“Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam.
SDP Na Ci Gaba da Ƙarfafa TsarukantaYa ce jam’iyyar na shirin fitar da manufofi masu amfani ga al’umma, inda za ta ba da dama ga matasa da mata wajen shiga siyasa da kuma samar da sabbin shugabanni masu nagarta.
Wannan furuci na shugabannin SDP na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa wasu manyan ‘yan siyasa na shirin shiga jam’iyyar don samun damar takarar shugaban ƙasa.
Duk da haka, jam’iyyar ta bayyana cewa ba za ta sauya tsarinta domin kowanne mutum ba, kuma za ta bi ƙa’ida wajen fitar da ‘yan takara a zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Alƙawari Shugaban Jam iyya takara
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya sheƙar da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban suke yi.
A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ta jawo ɗiga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaɓen 2027.
Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan ƙasar suke kokawa bisa yadda ake gudanar da mulki da kuma yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC.
NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaWannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai da nufin gano alƙiblar da siyasar Najeriya take shirin fuskanta.
Domin sauke shirin. Latsa nan