A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa
Published: 9th, March 2025 GMT
Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar adalci da zaman daidaito, kuma karin kasashe na rungumar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama.
Mutanen kasashen yamma su kan ce, “Moriya ta fi zumunta muhimmanci da dorewa”. Amma a ganin Sinawa, ya kamata abota ta dore har abada, kuma hakan zai tabbatar da moriyar kowa. Kamar dai yadda ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada, “Tarihi zai shaida cewa, wadanda suke rungumar kowa, su ne za su ci nasara. Hada kan juna don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, zai mai da duniyarmu ta zama ta kasa da kasa, tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga kowa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Mufti Na Masarautar Oman Ya Yi Kakkausar Suka Kan Masu Son Kulla Alaka Da H.K.Isra’ila
Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila
Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe.
A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya ce: “Abin mamaki ne yadda wasu kasashe ke son kyautata alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, alhali su kansu suna kallon wannan mahalukiya a matsayin wata kasa mai gushewa ko ba dade ko ba jima, al’ummarta dai suna son ci gaba da yakin ne kawai don ci gaba da wanzuwarta, in ba haka ba, babu wanda a can yake son ci gaba da zama a wannan kasa bayan sun ga cewa hakan ba ya cikin maslahar rayuwa.”
Al-Khalili ya ce: “Ta yaya wadanda suke da tushe zasu kulla alaka da gwamnati da zata gushe da hukuma wacce zata gushe ko ba dade ko ba jima.?
Babban Mufti na masarautar Oman ya kara da cewa: “Idan kana son sanin girman bala’i da girman masifa, to ka yi tunanin yadda alakarka zata kasance da mai dabi’ar dabbobi mai kashe fararen hula daga yara da mata da kuma tsofaffi, ta yaya zai kare maka naka hakkokin? Ya karkare bayanin da cewa: “Mutum ya halaka a cikin kwanakinsa na jarrabawa…idan baya iya bambance tsakanin mai kyau da maras kyau.