IRGC Ta Kaddamar Da Sabbin Makamai A Atisayen Da Take Yi A Halin Yanzu
Published: 20th, February 2025 GMT
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu.
Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare.
A jiya Laraba ne dai aka kaddamar da sabbin makamai masu linzamin wanda ya sami halartar manjo janar Muhammad Bakeri da shi ne babban hafasan hafsoshin sojan kasar Iran.
Shi kuwa janar Ali Kuhistani da shi ne mataimakin kwamandan rundunar ta IRGC a fagen kayan yaki, ya ce; Sabbin makamai sun kunshe da kayan aiki na zamani masu muhimmanci da aka hade su wuri daya.
Wannan dais hi ne karo na 19 da IRGC ke gabatar da atisayen mai yaken; Manzon Allah Mafi Girma”.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000
A ci gaba da hare-haren da dakarun Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, yanzu adadin Falasdinawan da suka kashe ya kai 60,034.
A cewar wasu alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, baya ga wannan, adadin wadanda aka raunata kuma a yanzu sun haura 145,870.
Ma’aikatar ta kuma ce har yanzu ana zargin akwai mutanen kuma da ke karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa, wadanda ba za a iya ciro su daga ciki ba.
Fiye da kaso daya cikin uku na mutanen yankin na shafe kwanaki ba su ci abinci ba, kamar yadda wani rahoton samar da abinci mai lakabin IPC na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar.
Rahoton ya ce ana samun karin hujjoji da ke nuna ana fama da yunwa da karancin abinci da kuma karuwar mace-mace masu alaka da yunwa a yankin da sama da mutum miliyan biyu da dubu dari daya ke rayuwa a cikinsa.
Hukumomi daban-daban na Majalisar Dinkin Duniya dai sun yi gargadin cewa ana fama da matsananciyar yunwar da aka kirkira da gangan a Gaza, inda a iya wannan watan, rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutum 63, dalilin yunwar.
Hukumomin dai sun dora wa Isra’ila duk alhakin matsalolin, kasancewar ita ta yi wa yankin kawanya ta kuma hana a shigar da kayan agaji.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce: “Abubuwa ne ga su nan a Zahiri, ba a boye suke ba. Falasdinawan da suke Gaza na cikin mawuyacin hali da tsananin bukatar agaji.
“Wannan ba wai gargadi muke yi ba. Gaskiya ce ga ta nan karara. Dole kayan agaji su ci gaba da kwarara. Abinci, ruwan sha, magunguna da man fetur dole su ci gaba da shiga ba tare da kowanne irin tarnaki ba,” in ji Guterres.