Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
Published: 11th, February 2025 GMT
Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Nasarawa Ya Ce Za Su Samar da Masana’antu Don Ayyukan Yi
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa hangen nesansa na ƙarfafa masana’antu a jihar shi ne domin ƙirƙirar ayyukan yi da kuma inganta rayuwar jama’ar jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnati ta Lafia, yayin da yake karɓar bakuncin sabbin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu aiko rahotann dake Jihar (Correspondents’ Chapel).
Ya ce baya ga jawo ‘yan kasuwa masu saka jari a fannin masana’antu da ma’adinai, gwamnatin sa tana kuma zuba jari mai yawa a harkar noma.
“Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ba ni farin ciki shi ne harkar noman shinkafa. Ka san muna da wata ƙaramar gona mai girman hektare 3,300 domin noman shinkafa.
Ina alfahari da gonar shinkafar mu domin mun fara girbi, kuma dukkan alamu sun nuna cewa amfanin gona a wannan kakar ya fi na bara, musamman a yawan amfanin da ake samu a kowace hekta,” in ji shi.
Gwamna Sule ya ce yana da cikakkiyar niyya ta ƙaddamar da aikace-aikace da shirye-shirye da za su tabbatar da amfanin kai tsaye ga jama’ar jihar.
A cewarsa, ɗaya daga cikin dalilan da ke haifar da kalubale da rashin tsaro a arewacin ƙasar, shi ne mutane da yawa ba su da abin yi.
“Ka san wannan shi ne ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo matsalar tsaro.
A da, lokacin da muke yara, akwai masana’antar yadi (textile) a Kaduna da ƙananan masana’antu a sassa daban-daban na arewa, mutane suna da abin yi.
Ba a cika jin labarin rashin tsaro ba, domin mutane suna zuwa gona, suna yin aikinsu da halaltattun hanyoyi,” in ji gwamnan.
Yayin da yake taya sabbin shugabannin ƙungiyar ‘yan jarida murna bisa nasarar rantsar da su, Gwamna Sule ya kuma bukace su su tsaya kan ƙa’idar aikin jarida ta gaskiya da adalci.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida na Jihar Nasarawa, Alhaji Abubakar Abdullahi, ya ce ziyarar ta kasance ne domin gabatar da sabbin shugabanni ga gwamna da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnati da ‘yan jarida.
Ya yaba wa Gwamna Sule bisa aikace-aikacen ci gaba da gwamnatin sa ke aiwatarwa, musamman gona mai girman hekta 3,300 a Jangwa, karamar hukumar Awe, wadda amfanin shinkafar ta za ta shiga kasuwa a ƙarƙashin sunan alamar jihar “NASACCO Rice.”
Ya kuma ambaci wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da gine-ginen gadar sama da ƙasa a Lafia, ayyukan gadar Keffi/Akwanga, sabuwar cibiyar ma’aikata ta jihar, da kuma biyan fansho da hakkokin ma’aikata a kan lokaci.
“Gwamnatinka tana ci gaba da nuna goyon baya ga ci gaban aikin jarida, kuma muna godiya da kyakkyawar dangantaka da muke da ita, tare da fatan za ta ci gaba da dorewa,” in ji shi.
Aliyu Muraki, Lafia.