Isra’ila Ta Bar Falasɗinawa Sun Fara Komawa Arewacin Gaza
Published: 28th, January 2025 GMT
Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
.কীওয়ার্ড: Falasɗinawa Isra ila yaƙi
এছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu
Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya.
Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — DalungSanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya.
“Mu a matsayimmu na ƙasa mai son zaman lafiya, muna roƙon ƙasashen da ke rikici da su zauna su tattauna maimakon su ci gaba da faɗa.”
Gwamnatin Tarayya ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya, musamman Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da su ɗauki matakai don hana yaɗuwar rikicin da kuma samo hanyar warware matsalar.
Sanarwar ta ƙara da cewa amfani da ƙarfin soji ba shi da amfani matuƙa, domin faɗa ba zai kawo sauƙi ba.
Najeriya ta ce a shirye ta ke ta bayar da taimako domin hana yaɗuwar rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.