2025-06-19@23:06:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5868

«Al ummar Musulmi»:

    Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta iya samun nasara a yaƙin da take yi da Iran ko da kuwa Amurka ba ta shigar mata ba. Sai dai Herzog ya shaida wa ABC News cewa kawar da barazanar nukiliyar Iran yana da muhimmanci ga “duniya mai ’yanci”, ciki har da Amurka. Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da Isra’ila — Birtaniya Da yake amsa tambayar ko me zai ce dangane da yiwuwar shigar wa ƙasarsa yaƙin da take yi da Iran da Shugaba Donald Trump ya yi iƙirari, Herzog ya ce “ina da cikakkiyar yarda a kan duk wani hukunci...
    Gwamnan ya ƙara da cewa: “Tinubu ya cancanci goyon bayanmu, kuma ba za mu daina yaba masa ba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke shawara kan ko zai shigar wa Isra’ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka. A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt ta karanto, Trump ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu. Waadin yanke shawarar da Trump ya bayar na zuwa ne bayan kwanaki ana rade-radin cewa Amurka za ta shigar wa Isra’ila yaƙin da ta ƙaddamar don ganin ta hana Iran mallakar makaman nukiliya. Trump dai ya shafe makonni yana bibiyar hanyar diflomasiyya don cimma yarjejeniyar nukiliya da Iran wadda ya soma tattaunawa da ita tun a wa’adinsa na farko a shekarar 2018. Sai dai duk da...
    Yau Alhamis, an bude bikin baje kolin kayayyakin kasar Sin da kasashen kudancin Asiya wato CSAE karo na 9, tare da taron cinikayyar kayayyakin shige da fice na Kunming na Sin karo na 29, wanda za a gudanar tsawon kwanaki 6, a cibiyar baje kolin kasa da kasa na tabkin Dianchi na birnin Kunming a lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Baje kolin CSAE na bana ya kunshi mahalarta daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa guda 73, da fiye da kamfanoni 2500 da ke baje kolinsu, kana da halartar dukkan kasashen kudancin Asiya da kudu maso gabashin Asiya. Baje kolin na wannan karo na ci gaba da amfani da taken “Yin hadin gwiwa da samun...
    A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar hanya. Indomie tun da dadewa tana da kaimin ciyarwa da abincin dake gina jiki da kuma cincidar Mafarkin kowanne yaro. Wannan dandalin na Indomie AI Career Generator ya tunkari wannan manufa, na taimakawa yara su fahimci ƙarfin gwiwarsu, su yi manyan mafarkai, kuma su san cewa makomarsu tana gab da su. “Indomie ta tallafa wa yarada dama wajen girma, koyo, da zama ababen Alfahari. Tare...
    A yau Alhamis, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar tana ba da muhimmanci sosai kan kiyaye kwanciyar hankali da tsaron bangaren masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kana tana kara hanzarta sake duba bukatun samun lasisin fitar da kayayyakin ma’adanai na “rare earth” masu daraja da ake sarrafa kayayyakin fasaha da su kamar yadda yake kunshe a tanade-tanaden dokoki da ka’idoji masu alaka da hakan. Mai magana da yawun ma’aikatar He Yadong, ya bayyana a wani taron manema labarai lokacin da yake amsa wata tambaya kan fitar da ire-iren wadannan ma’adanan cewa, kasar Sin ta amince da wasu bukatun da suka dace bisa doka, kuma za ta ci gaba da karfafa sake nazari da amincewa...
    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran, yana mai kiran da a biyo wa lamarin ta hanyar lalama. Mista Starmer ya ce akwai “mummunan hatsarin bazuwar” yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu. Ba zai yiwu mu bar Khamenei a raye ba — Isra’ila Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe Ya ƙara da cewa a baya an samu “jerin tattauna masu yawa da Amurka, kuma ina ganin wannan ita ce hanyar warware matsalar.” Kalaman nasa na zuwa ne yayin da sakataren harkokin wajensa, David Lammy ke shirin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio kan yadda za a taƙaita bazuwar yaƙin....
    Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz ya ce ba zai yiwu su bar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a raye ba. Israel Katz ya yi barazana ga Ayatollah yana mai cewa ya zama tilas ya ɗauki alhakin hare-hare da makamai masu linzami da Iran ta yi a kan wata cibiyar lafiya da ke kusa da Tel Aviv. Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Kafin harin an yi ƙoƙari kwashe marasa lafiya da dama, saboda a ceto rayukansu. Tuni dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci Cibiyar Lafiya ta Soroka da ke Beersheba da harin makami mai linzami na Iran ya...
    Shawara ta uka ita ce, hawa teburin tattaunawa da shawarwari ta zama babbar hanyar samar da mafita. Inda ya ce, dole ne mu yi tsayin daka wajen tabbatar babbar alkiblar da za a fuskanta kan warware matsalar nukiliyar Iran ta zama ta hanyar siyasa. Ta hudu, ya bayyana cewa kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya abu ne mai matukar muhimmancin gaske. Kuma ya kamata kasashen duniya musamman ma manyan kasashen da ke da tasiri na musamman kan bangarorin da ke rikicin, su yi kokarin yayyafa ruwa amma ba akasin haka ba. Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na son ci gaba da karfafa zantawa da gudanar da tsare-tsare da dukkan bangarorin, da kuma taka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar. Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya...
    “Za a sauƙaƙe hakan ne ta hanyar Bankin Raya kasa na KfW da Asusun Kalubalan Kasuwancin Afirka.”   An gudanar da bikin sanya hannun ne a ofishin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu, wanda ya wakilci Nijeriya.   Sakatare na farko kuma shugaban hadin gwiwar raya kasa a ofishin jakadancin Jamus a Nijeriya, Dr Karin Jansen, da wakilin bankin raya kasa na KfW, Gerald Keuhnemund, duk sun halarci rattaba hannun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar kasar Sin a taron birnin Geneva, ta shaidawa kungiyar cinikayya ta duniya WTO, cewa kasar ta fadada matakinta na rage harajin fito da take karba daga kasashe masu karancin karfin tattalin arziki, daga kaso 98 bisa dari zuwa kaso 100 bisa dari. A jiya Laraba ne tawagar ta Sin ta bayyana wannan albishir, inda ta ce baya ga janye dukkanin harajin fito baki daya, Sin ta sha alwashin kara aiwatar da matakai na ingiza cinikayyar hajoji, da karfafa kwarewar aiki, da aiwatar da kwasa-kwasai na horar da sana’o’in fasaha a kasashen Afirka masu raunin tattalin arziki. Kazalika, tawagar ta Sin ta ce wadannan matakai na da nufin samar da sabbin damammakin habaka ci gaban wannan rukuni na kasashen Afirka,...
    Dangane da sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar na cewa za ta maido da yin tambayoyi ga dalibai kafin a ba su biza kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta lura da batun, kuma tana fatan Amurka za ta aiwatar da kalaman shugaba Trump na maraba da daliban kasar Sin da su zo Amurka don yin karatu. Dangane da wani rahoto da wata cibiyar bincike ta kasar Switzerland ta fitar, inda ta bayyana cewa, matsayin karfin yin takara na yankin Hong Kong na Sin ya karu zuwa matsayi na uku a duk fadin duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan na nuni da matsayin Hong Kong na musamman da kuma alfanun da ake da shi, da kuma...
    Brig.-Gen. Abu-Mawashi ya kara da cewa an kama ‘yan ta’adda 14,138 da sauran masu aikata laifuka yayin da aka ceto mutane 5,365 a cikin wannan lokaci.   Abu-Mawashi ya ci gaba da cewa, sojojin sun kwato daruruwan makamai da kuma harsashi da yawa duk acikin wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na ziyarar aiki a cikin Jihar Kaduna. Shugaba Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Uba Sani ya aiwatar a tsawon shekara biyu da ya yi yana mulkin jihar. Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio Wasu daga cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da: asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya. Daga nan kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i, da kuma motocin sufuri masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100. A cikin waɗanda suka yi wa Shugaba...
    A shekaru biyu da suka wuce, shugaban kasar Sin da takwarorinsa na kasashen nan biyar sun dasa wasu bishiyoyin ruman guda shida a birnin Xi’an, wadanda yanzu haka cike suke da furanni tare da alamanta hadin gwiwar kasashen mai cike da kyawawan nasarori, wadanda kuma suka shaida cewa, “hannu daya ba ya daukar jinka”, hada karfi da karfe ne zai kai ga inda aka dosa, kuma ba wanda ke iya cin nasara daga faduwar wasu, kuma za a iya tabbatar da nasara ga juna ne kurum idan aka zama tsintsiya madaurinki guda. Yanzu haka, duniyarmu na fama da rikice-rikice da kariyar ciniki da ra’ayi na kashin kai da kuma siyasar nuna fin karfi. Amma bai kamata a mai da hannun...
    Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025. Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a ranar Talata. Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio Ba Atiku kaɗai ba ne matsalar PDP — Gwamna Lawal Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce NAHCON tare da hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, da kuma masu jigilar jiragen sama na shekarar 2025 suna yin duk abin da za su iya...
    Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.” Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma hakan ya saɓa da Sashe na 391 na Dokar Laifuka 89, Dokokin Tarayya na shekarar 1990. Hukuncin laifin yana ƙarƙashin Sashe na 392 na wannan doka. A wani tuhumar daban, an zargi Sanata Natasha da yin irin waɗannan kalaman game da Akpabio a cikin wata tattaunawa ta waya da wata Sandra C. Duru a Abuja, a ranar 27 ga watan Maris, 2025. An ƙara tsaurara...
    Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna. Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba. Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Ya halarci bikin kuma hakan ba yana nufin ya goyi bayan wata jam’iyya ba ne. Ƙungiyarsa ta nanata cewa Sambo yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma labarin sauya sheƙar nasa ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da ƙoƙarin cimma wasu muradu na siyasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Babbr Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, kan Naira miliyan 50. Muna tafe da karin bayani…
    Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa wasu ’yan Najeriya su biyar hukuncin daurin shekaru 159 bisa samun su da da laifin damfarar Amurkawa sama da 100. Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin damfarar kamfanoni da hukumomin gwamnatin kasar kudin da yawansu ya kai Dala miliyan 17, kwatwankwacin Naira biliyan 27 da miliyan 200. Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen shari’a na kasar ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Laraba, mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin Babban Lauyan gwamnati na gundumar gabashin Texas, Ray Combs. ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a Zamfara Sanarwar ta ce mutanen da aka yanke...
    Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan zarginta da karɓar bashi na dala miliyan 6.6. Gwamnatin Kano ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba gaskiya ba ne face tsantsar siyasa. Ko da yake masarautar ba ta danganta ƙwace sarautar da wannan suka da Alhaji Usman ya yi ba, lokacin da aka ɗauki matakin ya haifar da zargi da cece-kuce a tsakanin jama’a. Daga kanmu, magana...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsalar da ke addabar jam’iyyar PDP ba ta tsaya kan Atiku Abubakar kaɗai ba, face tana da nasaba da girman kai tsakanin shugabannin jam’iyyar. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Gwamna Lawal ya ce: “Kowa yana da nasa matsalar; ba kan Atiku Abubakar kawai ba ne; ta wuce hakan.” An ɗaure mutum 7 kan yi wa ɗan sanda rauni a Kano ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina “Matsala ce daga cikin gida… Na ga matsalar tana da alaƙa da girman kai, ba a bar kowa a baya ba.” Da aka tambaye shi ko yana daga cikin masu haddasa matsala a cikin jam’iyyar, ya amsa cewa yana ciki. Gwamna...
    Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar. Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar. Taron na...
    Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba. Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu haka fargaba ta karaɗe yankin, yayin da jama’a ke roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan matsala da ta dabaibaye rayuwarsu da amfanin gonarsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kashe akalla manoma 20 da wasu mutum uku da kuma wani dan sinitiri a jihar Katsina. An kashe mutanen ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai karamar hukumar Kankara, daya daga cikin yankunan da suka fi fama da kalubalen tsaro a jihar. A cewar wani mazaunin yankin da bai amince a bayyana sunansa ba, “Kimanin kwanaki shida da suka gabata ’yan bindiga suka kai hari kauyukan Yargoje, Kwakware, Danmarke, Gidan Dawa da kuma Burdugau. Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a Zamfara NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na “Sun kashe kusan manoma 20, sun sace wasu sannan suka sace shanun da manoman ke amfani da su wajen huda...
    Al’ummar garin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, sun gudanar da sallar roƙon ruwa bayan da aka shafe kwanaki ba tare da an samu ruwan sama ba. Mutane da dama sun fara nuna damuwa saboda har yanzu babu ruwa ba, duk da cewa an shiga lokacin damina tun da daɗewa. NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi Wasu manoma da ke jiran ruwa domin su yi shuka sun ce har zuwa ranar Laraba sun fito domin roƙon Allah Ya saukar da ruwa. Babban limamin garin Kaura, Malam Badamasi, ne ya jagoranci sallar. Ya ce sun ga dacewar yin wannan addu’a ne domin tun mako...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan. A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan...
    A watan Afrilun bana, wata farar mota kirar bas mai tsawo mita 12, ta yi tafiya a kan titunan Ashgabat, hedkwatar kasar Turkmenistan. Bas din da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera ta dace da ma’aunin kiyaye muhalli da kasar ta tanada, kuma tana dauke da na’urar ba da jagorancin sufuri mai amfani da tauraron dan Adam, da na’urar biyan kudi ta yanar gizo, matakin da ya bullo da sabuwar hanyar zirga-zirga ga jama’ar wurin. A wannan shekara, Sin za ta samar da irin wannan bas har 700 ga Ashgabat, matakin da zai biya bukatun zirga-zirgar jama’ar kasar da yawansu ya zarce miliyan 1. Tun da aka bude taron koli na Sin da kasashen shiyyar tsakiyar Asiya karon farko...
    Idan dai za a iya tunawa, a baya an kai hari gidan dangin Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 15 ga Afrilu, 2025, ba tare da an kama ko daya daga cikin maharan ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta kira taro karo na 63 mai taken “Ba da tallafin ciniki” a jiya Talata a birnin Geneva. Yayin da aka tattauna bisa ajandar “Makomar hadin gwiwar kasashe masu tasowa da saurin bunkasuwa”, Sin ta yi cikakken bayani kan dabaru, da fasahohi da Sin take da su a fannin tallafawa sauran kasashe masu tasowa wajen gina manyan ababen more rayuwa, da gaggauta karfin samar da tsare-tsaren cinikayya, matakin da ya samu karbuwa matuka daga mahalarta taron. A bangaren nahiyar Afirka, kasar Mozamqiue ta darajanta kokarin da Sin take yi na karawa kasashe masu tasowa kwarin gwiwar gina ingantattun manyan ababen more rayuwa, da gaggauta karfin samar da tsare-tsare, karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kada a kuskura a shiga tsakanin yaƙin da Iran da Isra’ila ke fafatawa ta hanyar amfani da ƙarfin soji.  Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gargadi kan duk wani “shiga tsakani na soji”, a yankin Gabas ta Tsakiya, inda manyan abokan gaba Isra’ila da Iran ke musayar wuta a rana ta shida. Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi Nijeriya za ta fara fitar ta tataccen mai zuwa Asia — Matatar Dangote Ita ma ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci bangarorin biyu, da su kare fararen hula yayin da adadin mace-mace da jikkata ke ci gaba da karuwa. Babbar sakatariyar ƙungiyar ta kasa da kasa, Agnes...
    Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari.   Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya...
    Rundunar sojin Nijeriya ta sanar dakashe gomman ’yan ta’adda na ISWAP da Boko Haram da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojin ruwan ƙasar a yankin Tafkin Chadi. Hakan dai na kunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba wadda ta ce ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojojin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, inda suka yi ƙoƙarin lalata sabbin motocin tafiya a fadama waɗanda gwamnatin Jihar Borno ta saya domin yashe hanyoyin ruwa. Nijeriya za ta fara fitar ta tataccen mai zuwa Asia — Matatar Dangote HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe Sai dai jami’ai a sansanin sojin ruwan Nijeriya da ke Tafkin Chadin...
    Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha mai tsafta wanda kamfanin CGCOC na kasar Sin ya tallafa wajen gudanar da shi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, ta yin aiki tukuru a fannin samar da ababen more rayuwa, da kai tsaye za su inganta rayuwar al’ummun kasar. Shugaba Tinubu ya bayyana aikin a matsayin muhimmin mataki na tabbatar da al’ummun birnin sun samu ruwa mai tsafta, mai dorewa kuma isasshen a gidaje da hukumomi, da dukkanin sassan birnin. Ya kuma godewa gwamnatin kasar Sin da kamfanin CGCOC, bisa hadin gwiwarsu wajen tabbatar da nasarar aikin. Yayin da yake nasa tsokaci kuwa a bikin kaddamar da aikin, mukaddashin jakadan Sin...
    Gwamnan babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce kasar za ta samar da cibiyar kasa da kasa ta gudanar da hada-hadar kudin RMB na dijital.   Pan, wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, yayin taron Lujiazui da ya gudana a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin, ya ce makasudin kafa cibiyar shi ne bunkasa hada-hadar kudin RMB na dijital tsakanin sassan kasa da kasa, da ciyar da hidimomin raya kasuwannin hada-hadar kudade gaba, baya ga tallafawa kirkire-kirkire a fannin hada-hadar kudaden dijital. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    A karon farko Nijeriya za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyyar Asia kamar yadda wata majiya daga Matatar Dangote ta sanar. Majiyar ta ce wani jirgin ruwan dako mai ɗauke da tan 90,000 na man fetur zai yi jigilar daga Matatar Dangote da ke Nijeriya zuwa nahiyar Asia. HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti  Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ambato majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta tana cewa “yanzu jirgin ruwan Mercuria zai tafi Asia a ranar 22 ga Yuni.” “Muna sayar da kayanmu ne ga waɗanda suka yarda su ba mu farashi mafi yawa. Mai saye na da haƙƙin...
    Aiki ceton, ya samu hadin gwiwar kungiyoyin ceto da suka hada da Red Cross da Hukumar Kula da Ruwan Kogin (NIWA) da jama’ar garin Yauri.   A ranar Laraba, an yi jana’izar Mutane uku, a garin Hikiya da ke karamar hukumar Rohiya a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada. Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare...
    Sauran sun hada da: Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun.   Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a kan karagar mulki, sannan gwamnatin jihar ta siya musu motocin alfarma.     Bincike ya kuma nuna cewa, motocin da aka ce kudinsu ya kai Naira biliyan 2.5. Bayan sun sauka akan mukaminsu, sun tafi da motocin kuma duk kokarin da aka yi na su dawo da su, lamarin ya ci tura.   Sai da gwamnatin jihar ta sake sayo wa ‘yan majalisar na yanzu motocin da kudinsu ya kai kimanin...
    An gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar Kazakhstan, daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Yunin shekarar 2025, don halartar taron koli karo na biyu na Sin da tsakiyar Asiya. A karshen ziyarar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da lamarin. Wang Yi ya ce, babban abin da ya fi daukar hankali a wannan taro shi ne sanarwar da shugaba Xi Jinping ya yi ta “Ruhin Sin da Tsakiyar Asiya”. Inda shugabannin kasashen yankin tsakiyar Asiya suka amince baki daya kan kiyaye wannan ruhi, da inganta tsarin kasar Sin da tsakiyar Asiya don samun sabon babban ci gaba. Bugu da kari, dangane da halin da ake ciki a yankin...
    Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara asibiti da ke Makurdi, Babban Birnin Jihar Benuwe, domin duba waɗanda da suka jikkata a hare-haren da ‘yan bindiga suka jihar. Shugaban ya je ne domin ganin irin ɓarnar da aka yi, tare da nuna alhini da goyonnsa baya ga al’ummar jihar. Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti  Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato Hotunan ziyayar sun nuna Tinubu yana duba da waɗanda abin ya shafa. Go hotunan a ƙasa:
    A yayin ƙaddamar da asibitin ƙwararrun, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya buƙaci gwamna Lawal da ya ci gaba da gudanar da ayyukan ceto har sai Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin manyan jihohin Nijeriya.   Tsohon shugaban ƙasar ya ce: “A yau ina jihar Zamfara ne domin na ga ingantacciya, wadda ta ci gaba, mai ci gaba kuma sabuwar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin ka.   “Ga mu nan. Abubuwa biyu sun ba ni mamaki: Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa kun samar da na’urorin CT scan da MRI Machine, na san wasu asibitocin koyarwa ba su da CT scan da MRI, wasu kuma suna da shi amma ba sa aiki. Ku ga na ku, yana aiki ga al’umma.   “Na...
    Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka. Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kai ziyara Jihar Benuwe domin jajanta wa mutanen jihar bisa hare-haren da suka faru a wasu ƙauyuka kwanan nan. Ya je ne domin nuna alhininsa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattaunawa da shugabanni don nemo mafita mai ɗorewa. Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi A yayin ziyarar tasa ta yini guda, Shugaba Tinubu ya fara ne da ziyartar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwe, inda ta duba waɗanda suka jikkata. Shugaban ya shirya ganawa da iyalan waɗanda aka kashe, da waɗanda suka rasa muhallansu, da kuma shugabannin al’umma. Hakazalika, Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki s jihar,...
    Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta bayyana cewa ta shirya zama da ’yan bindiga domin tattaunawa idan har suna da niyyar ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya. Wannan bayani ya fito ne daga Hadimi na Musamman kan Harkokin Tsaro na Gwamna Ahmed Aliyu, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya). Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana Hadimin ya ce gwamnatin jihar na son tattaunawa don samar da zaman lafiya fiye da ci gaba da tafka yaƙi. Gwamnatin ta ce a tarihi, an fi samu damar warware rikice-rikice da dama ta hanyar yin sulhu, ba ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai ba. Saboda haka, jihar za ta iya tattaunawa...
    Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan ziyara a matsayin gwada gwamnati kan yadda za ta shawo kan matsalolin tsaro, musamman a jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da na ƙabilanci. Kisan da aka yi a Yelwata, wanda shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren, ya janyo suka damuwa a faɗin ƙasar tare da ƙara matsin lamba ga shugaban ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa don tabbatar...
    A ci gaba da yakin da suke yi da ’yan ta’adda, sojojin Najeriya sun samu nasarar jikkata jagoran kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi a dajin Sambisa. Bayanai sun nuna sojoji sun sami nasarar ce bayan wani gagarumin harin da suka kai ta sama a wani sabon sansani na ’yan ta’addan da ke dajin Baikee a yankin Sambisa a Jihar Borno. Dakarun rundunar da ke karkashin Operation KALACHEN WUTA, wanda bangare ne na rundunar sojojin saman Najeriya da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ne suka kai harin. Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu Majiyoyin sojojin Najeriya da ke...
    Masana sun yi gargadin cewa yakin da ake gwabzawa a tsakanin Isra’ila da Iran zai iya shafar farashin man fetur a duniya kuma hakan zai iya yin illa ga tattalin arzikin Najeriya. Masanan na cibiyar Commercio Partners da ke Legas sun  bayyana fargabar ce a cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar mai taken: “Farashin kayayyaki ya sauka a Najeriya a watan Mayu, amma akwai matsala a nan gaba” wanda aka wallafa shi ranar 16 ga watan Yunin 2025. A cewar rahoton, rikicin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya zai iya rage yawan man fetur din da ake samarwa a duniya wanda kuma zai kai ga tashin farashinsa a kasuwanni. Ma’aikatan Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna za...
    Kungiyoyin ma’aikata na Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, Kafanchan sun bayyana aniyarsu na fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku. Sun ce za su shiga yajin aikin ne daga ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Wannan matakin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da suka yi bai wa gwamnatin jihar, wanda zai kare ranar Laraba, 18 ga watan Yuni. Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu Ambaliyar Mokwa: Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja Aminiya ta rawaito cewa kungiyoyin da suka hada da na Kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi (COEASU), SSUCOEN da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Kwalejojin Ilimi ta Najeriya (SSUCOEN) da Kungiyar Ma’aikatan da ba na...
    A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda. Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000. Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa Masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, sannan ya sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka. Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja. A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar kudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka. Ambaliyar Mokwa: Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Kudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a fadin kasa, kafin...
    Wani mazaunin yankin, Abdullah Zuru, ya ce yankin ya samu zaman lafiya a baya, inda manoma suka koma gonakinsu kafin wannan mummunan hari. Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba dangane da harin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu akwai sama da mutum 700 da suka bace ba gan su ba tun bayan mummunar ambaliyar ruwan da aka yi a karamar hukumar Mokwa da ke jihar. Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi babban dogarin tsohon Shugaban Kasa marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayin ziyarar jaje kan ambaliyar a Minna ranar Talata. Gwamnan, wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta ya kuma ce akalla mutum 207 ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan gidaje sama da 3,000 ne suka rushe. DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bom “Sama da...
    “Da farko mun ɗauka yana wasa ne, amma kafin wani ya kai ɗauki, ya riga ya kunna wa kansa wuta.” Wata mazauniyar yankin, Aisha Salisu, ta ce yana matashin yana shaye-shaye. “Ba ya cikin hayyacinsa. Ana jin warin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, kuma yana karkarwa da ihu,” in ji ta. Mutane sun yi ƙoƙarin taimaka masa. Wasu sun ja shi zuwa cikin ruwan da ke wata magudanar ruwa a gefen hanya, amma wutar ta riga ta yi masa ƙone sa. “Abun ya zama kamar fim kuma mai ban tsoro,” in ji wani direban adaidaita sahu mai suna Ibrahim Jafar. “Ko bayan da suka jefa shi cikin ruwan, wutar ba ta daina ci nan take ba. Fatar jikinsa duk...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya.   Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya. Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya. Kazalika a kwanakin nan wani hari da aka kai a wasu yankunan jihar Binuwe yayi sanadiyyar halakar mutane da dama, wadda hakan ya jawo...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A cewar Omodara, wadanda ake zargin sun hada da ‘yan asalin jihar da ake zargi da taimakawa ayyukan ‘yan bindiga ta hanyar samar musu da kayan aiki kamar abinci, ruwan sha, da sauransu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin kasashe biyar na tsakiyar Asiya sun halarci bikin rattaba hannu tare da sanya hannu kan yarjejeniyar Astana ta taron kolin kasar Sin da yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, da kuma yarjejeniyar kyakkyawar makwabtaka da abota da kuma hadin gwiwa na dindindin. Har ila yau, sun kuma halarci bikin kaddamar da cibiyar hadin gwiwa da dandalin tattaunawa na tsakiyar Asiya da kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da kumbo mai daukar mutane. Wannan ita ce nasara irinta ta biyu da Sin ta samu a wannan bangare, bayan shekaru 27 da suka gabata, da samun nasara ta farko a aikin gwajin da ta gudanar a shekarar 1998. Aikin gwajin tserewar da aka gudanar ya kasance muhimmin mataki na ba da tabbaci ga rayukan ’yan saman jannati, wato idan an gamu da hadari ko matsala...
    Borussia Dortmund ta soma buɗe wasanninta na gasar FIFA Club World Cup da canjaras a karon-battar da ta yi da kungiyar Fluminense ta Brazil a ranar Talata. Ana dai ganin babbar kungiyar da ta zama gagarabadau a Rio de Janeiro Fluminense a matsayin mafi hatsari a rukunin F wanda ya kunshi har da kungiyar Ulsan HD ta Koriya ta Kudu. Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump An dai rika kai wa juna hari a yayin wasan da suka barje gumi a filin wasa na Metlife da ke East Rutherford a wajen birnin New York, sai dai mai tsaron ragar Dortmund, Gregor Kobel...
    Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF. An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53 Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da...
    Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayayyakin noma ga magidanta 1,000 da suka hada da ‘yan gudun hijira daga Mandunari da ke karamar hukumar Gujba da sauran al’ummomin da suke zaune a yankin. Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke Damaturu, Buni ya bayyana cewa, duk da cewa al’ummomin Mandunari ya kasance su ne yankin al’umma guda daya tilo a jihar Yobe da har yanzu ba a sake tsugunar da su ba, al’ummarta sun nuna jajircewarsu na komawa gidajen kakanninsu. Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da dawowar duk ‘yan gudun...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu. Wannan na zuwa ne yayin da Trump din ya gargadi Iran kan da kada ta kai harin makamai masu linzami kan fararen hula ko kuma sojojin Amurka, yana mai cewa hakurinsu na karewa. Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth mintuna kadan bayan wannan sako, Trump ya rubuta cewar Iran din ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba kawai. Rahotanni a...
    Daga karshe Musa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.   Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 200 ne aka kashe a wani hari da aka kai a Yelwata da ke karamar hukumar Guma, wanda galibi ya hada da ‘yan gudun hijirar da ke neman mafaka a wani cocin Katolika na yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yawan masu karanta adabin da aka dora a shafin intanet na kasar Sin ya karu zuwa miliyan 575, lamarin da ya nuna yadda ake samun karuwar karanta labarai da rubutun zube ta fasahar zamani a fannin al’adun kasar. Masu karatu da aka haifa bayan shekarar 2000 su ne suka kara yawan ci gaban da aka samu a baya-bayan nan, wadanda suka dauki kusan kashi hudu na dukkan masu karatu a shafin na intanet, kamar yadda wani rahoto da kungiyar marubuta ta kasar Sin ta fitar a yau Talata ya bayyana. Bisa bayanan da aka samu daga manyan dandalolin adabi na intanet guda 50 a fadin kasar Sin, rahoton ya kiyasta cewa, masana’antar adabin ta samar da kudin shiga kusan yuan...
    Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta shirya tsaf wajen aiwatar da soke haraji da kashi 100 bisa 100 a kan kayayyakin kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar jakadanci da kasar ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin raya tattalin arziki.   A yau, wani jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya gabatar da wani batu da ya dace da hakan. Inda ya bayyana cewa, a mataki na gaba, ma’aikatar kasuwanci za ta yi aiki tare da sassan da abin ya shafa, wajen inganta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki don samun ci gaba na bai-daya tare da kasashen Afirka bisa ka’idojin tuntubar juna da samun moriyar juna dai-dai-wa-daida....
    Kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun yi iƙirarin cewa ƙasar ta kai hari kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad). Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ruwaito cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya. Kamfanin ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda hedikwatar ta Mossad ke ci da wutan ne bayan harin makamai masu linzami ne da Iran ta kai mata. Kafar yaɗa labarai ta Tehran Times ta ruwaito cewa hare-haren na IRGC sun ƙona wani ɓangare na cibiyar Aman, wanda wani ɓangare ne na ginin hukumar leƙen asirin asirin sojin Isra’ila ta Aman, da ke Glilot. An garzaya da...
    Ga cibiyoyin CBT, Oloyede ya ce dole ne a gargadi wadanda ke da hannu sannan a nemi su sanya hannu kan takardar yarjejeniya. Kuma bayan yarjejeniyar, za a kuma buƙaci su ba da shaidar horar da masu rajistar daliban.   Da yake karin haske kan shawarwarin, Oloyede ya ce hukumar ba za ta yi la’akari da duk wani uzuri ba daga cibiyoyin da abin ya shafa a nan gaba ba, duk da ikirarin da suke yi na rashin sani, don haka akwai bukatar su samu horon da ya dace a jami’o’in gwamnatin tarayya da ke kusa da su kafin JAMB ta kara amincewa da su.   Cibiyoyin CBT da abin ya shafa da aka gayyata taron sun hada da Misau...
    Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A. Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe. Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bom A cewar kafofin watsa labarai na Italiya, Palermo ta biya Pisa kusan dala miliyan 1.1 wajen ɗaukar Inzaghi. Pisa dai ta ƙare gasar Serie B a mataki na biyu a ƙarƙashin jagorancin kociyan mai shekaru 51, lamarin da ya ba ta nasarar haurowa gasar Serie A karon...
    A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron koli na kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu. A cikin jawabinsa, Xi ya ce, yayin da kasar Sin da kasashe biyar na yankin tsakiyar Asiya ke tafiya kan hanyar samun ci gaba a cikin dogon lokaci, sun kafa “Ruhin Sin da kasashen tsakiyar Asiya” na “Mutunta juna, da amincewa da juna, da moriyar juna, da taimakon juna, da inganta zamanantarwa tare ta hanyar samun ci gaba mai inganci”. Yayin da ya ambaci yanayin rashin kwanciyar hankali da duniya ke fama da shi, ya ce ta hanyar tabbatar da adalci ne za a iya cimma burin kare zaman lafiya, da samun ci...
    Sinawa tun zamanin baya na ganin cewa, samun dadi ga kowa shi ne dadi na gaske. A zamanin yanzu, kasar Sin ba kawai take jin dadin sauye-sauyen da ke faruwa a sassan hamada na kasar ba, hatta ma tana fatan ganin karin yankunan hamada sun zama dausayi a fadin duniya. Don haka, take kokarin bayar da fasahohinta ga kasashen Afirka da su ma suke fuskantar kalubalen kwararar hamada. Bisa nazarin da masanan Sin da kasashen Afirka suka yi, sun gano cewa, fadin sassan hamada a yankin Sahel ya ragu daga kaso 72,31% zuwa 69.23% tsakanin shekarar 2000 zuwa ta 2020. Daga Taklimakan zuwa Sahara, karin abubuwan al’ajabi na ci gaba da faruwa bisa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta...
    Akalla mutane 20 sun mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani rikicin ƙabilanci da ya auku a wani lardi na gabashin kasar Chadi. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa ta ƙasar ta fitar, ta ce fadan ya barke ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni a yankin Molou na lardin Ouaddai da ke gabashin kasar. An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran Tankokin Isra’ila sun kashe mutum 51 a wurin karbar abinci a Gaza Wata majiya ta ce rikicin ya samo asali ne bayan da matasan Zaghawa biyu dauke da makamai suka sace babur na wani dan kabilar Ouaddai a ranar Talata, lamarin da ya haddasa kazamin rikici. Bayanai sun ce rikicin...
    Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin ƙasar Indonesiya, bayan da ya ɗauko alhazan da daga birnin Jidda na ƙasar Saudiyya. ’Yan sanda ƙasar Indonesiya sun ce an yi nasarar fitar da ɗauƙacin fasinjojin jirgin su 442 a filin jirgi da ke lardin Sumatra ta Arewa. Ma’aikatar Sufuri ta ƙasar Indonesiya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne bayan samun wani saƙon imel cewa an sanya bom a jirgi. Sarki ya...
    Isra’ila ta tabbatar cewa an garzaya da ’yan ƙasarta aƙalla 154 asibiti bayan sabbin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kawo mata. Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce aƙalla mutum huɗu daga cikin waɗanda aka kai asibitin suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, wasu biyar kuma na samun kulawa ta musamman saboda tsananin tashin hankali. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna cewa mutum 130 daga cikin majinyatan sun samu raunuka marasa tsanani a sakamakon hare-haren. Wannnan na zuwa ne a yayin da Iran ta ci gaba luguden rokoki a matsayin ramuwar gayya a sassan Isra’ila a a ranar Talata. Isra’ila ta ce Iran ta lashe mata mutane akalla 24. A ɗaya ɓangaren kuma Iran cewa harin tsokana da Isra’ila ta kai mata...
    Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa gwamnatin Jihar Katsina na ƙoƙarin sasantawa da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar. Wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke Jibia, Batsari da DanMusa sun amince da zaman lafiya tare da miƙa makamansu. Sai dai wannan hari na baya-bayan nan ya sa al’umma sun fara shakkar ko zaman lafiyar zai ɗore. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tankokin yaƙin Isra’ila sun i kashe kimanin mutun 51 a yankin Khan Younis da ke Zirin Gaza, a yayin da mutanen suke tsaka da karbar abincin tallafi. Jami’ain lafiya sun sun ce mutum 51 sun mutu, wasu 200 sun samu raunuka — 20 daga cikinsu suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai — bayan harin. Sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafiya muni da sojojin Isra’ila suka kai a baya-bayan nan a yayain da Falasdinawa ke kokarin samun abinci domin su rayu. Bidiyon lamarin da suka karade kafofin sada zumunta sun nuna wasu gomman gawarwaki da ake zargin tankokin yakin Isra’ila sun mutsuttsuke a kan titi a Khan Younis. Shaidu sun bayyana cewa sai da sojojin Isra’ilan suka sa mutanen suka...
    Hukumomin Isra’ila na ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile tasirin harin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila.  Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game da lamarin. Ya bayyana haka ne a yayin da yake hawa jirgi domin barin ƙasar Kanada, inda ya halarci taron ƙasashen G7. A yayin taron, shugabannin ƙasahen sun bayyana Iran a matsayin barazana, da bai kamata a bari ta mallaki makaman nukiliya ba. A ɗaya bangaren kuma sun bayyana ’yancin Isra’ila na kare kanta. Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan harin Iran Sarki ya...
    “Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba. Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa. “Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara...
    Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata. Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke ɗaukar zafi tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji. Bazan Group ya bayyana harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi. Harin na Iran ya kuma halaka ma’aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka sanar. Wannan na faruwa a ci gaba hare-haren ramuwar gayya da makamai...
    Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami. Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa wa matansa da ’ya’yansa duka a yankin Oke Agbe, da ke shiyyar Akoko a Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa a Jihar Ondo Jihar Ondo. Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta bayyana cewa, “Basaraken yankin ya yi Musulmin tara da aka ci zalinsu tara, saboda sun yi ihu tare da zagin dodannin, maimakon su riƙa yin kuka suna roƙon dodannin. “Basaraken ya umarci matan limamin su...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
    Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
    Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
    Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
    A wani gangamin magance aikata laifukan zamba da damfara ta shafukan intanet da kasar Sin ta kaddamar a fadin kasar baki daya, ‘yan sandan kasar ta Sin sun fatattaki laifuka 294,000 a shekarar 2024, inda suka kama mutane da dama da ake zargi ciki har da shugabanni gungu-gungu fiye da 570, da masu samar musu da kudi, da kuma kasurguman da ke da hannu a wannan ta’asar. ‘Yan sanda sun durfafi cibiyoyin sadarwa na masu aikata laifuka da ke ba da haramtaccen tallafi ga aikata ayyukan zamba a kasashen ketare. A cewar ma’aikatar kula da tsaron al’umma, wadannan kungiyoyin sun tafka ta’asa masu yawa da suka hada da tallata laifukan a shafin intanet, da satar kudi, da amfani da fasaha,...
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin. Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar  nan ta garkuwar...
    Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo ƙarshen rikicin ne. A wata hira ta tsawon minti 20 da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi, Netanyahu ya kare matakin farmakin da ƙasarsa ta kai wa Iran, inda ya kwatanta jagoran addini Khamenei a matsayin wani sabon Hitler na wannan zamani. Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan sisaya ta satar kuɗi — EFCC Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe A yayin hirar, duk wata tambaya da aka yi masa game da ko Shugaban Amurka Donald Trump ya sahale...
    A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev gabanin taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na biyu. Kazalika, daga bisani duk dai a yau shugabannin biyu za su halarci bikin musayar rubutaccen daftarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kazakhstan. Xi ya isa Astana, babban birnin Kazakhstan yau Litinin, domin halartar taron koli karo na biyu tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin. Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar  nan ta garkuwar...
    Za a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a lokacin ziyarar shugaban ƙasa. Tun da farko, Tinubu ya yi Allah-wadai da rikicin da ke faruwa a Benuwe, inda ya yi kira da a zauna lafiya. Haka kuma, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a sanadin rikicin. Tinubu ya shirya kai ziyara Jihar Kaduna a ranar Laraba domin ƙaddamar da ayyukan gwamnatin jihar, amma yanzu ya ɗage ziyarar zuwa ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya soke ziyarar aiki da ya shirya zuwa Kaduna, a maimakon haka zai ziyarci Jihar Benuwe domin jajanta wa al’umma sakamakon kashe-kashen da aka samu a jihar a baya-bayan nan. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin. Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Tinubu ya bayar da umarnin binciken hare-haren Benuwe Kakakin ya ce Shugaba Tinubu zai kai ziyarar ce a ranar Laraba domin duba halin da jihar ke ciki bayan kashe-kashen da aka samu a ’yan kwanakin nan a jihar. Haka kuma, a yayin ziyarar, shugaba Tinubu zai gana da masu ruwa da...