2025-11-05@11:40:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8

«Ayatollah Khamenei Ya»:

    Limamin da ya jagoranci sallar juma’ar birnin Tehran ya bayyana cewa: Shugaban Amurka Trump ɗan ta’adda ne kuma mai fafutukar yada ayyukan ta’addanci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’ar birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyed Ahmad Khatami, ya yi magana game da laifukan Amurka a cikin hudubarsa, yana mai cewa: Shugaba Trump ɗan ta’adda ne kuma mai haɓaka ayyukan ta’addanci a duniya. Ayatullah Khatami ya yi tambayar cewa: “Wa ya kashe shahidin Iran Qasim Sulaimani? Ba Amurkawa ba ne suka kashe shahidi Tehranchi ba, kuma suka kashe shahidi Abbasi. Hakika Amurka ce ‘yar ta’adda kuma mai haɓaka ayyukan ta’addanci. Wa ya ƙirƙiri kungiyar ta’addanci ta ISIS? Saboda haka, ikirarin Amurka na cewa tana son yaƙi da...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, zai gabatar da jawabi ga mutanen kasar Iran nan gaba kadan, saboda shigowar makin tsaro mai tsarki, inda ake saran zai tabo al-amura da suka shafi tsaron kasar da kuma siyasar kasa da kasa. Makon tsaro dai shi ne makon da aka fara yakin tsaron kasar mai tsari wanda ya zama masomin yakin tsaron na shekaru 8 tare da gwamnatin Ba’ath ta kasar Iran karkashin shugabancin Saddam Hussain a lokacin An fara yakin ne a ranar daya ga watan Mehr shekara 1359 wato a shekara 1980 har zuwa shekara 1988. Har’ila yau ana saran zai yi Magana kan sabbin al-amura da suke tasowa a cikin gida. Share...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta. Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta...
    Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ganawarsa da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a jiya Laraba a birnin Qom mai alfarma Ayatullah Makarem Shirazi ya yi ishara da yakin tunani da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka yi kan Iran yana mai cewa: Wadannan makiya sun yi zaton za su haifar da rudani ta hanyar kai...
    Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehra mya bayyana cewa: Hukuncin shari’a da ya hau kan Trumpm da Netanyahu shi ne kisa Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau ya bayyana cewa: Amurka da karen da suka horar sun yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma wannan wauta ce. Hakika dokar Musulunci ta Trump da Netanyahu ita ce mutuwa. Sun kashe mutane fiye da 55,000 a Gaza. Su suka kai Qasim Sulaimani da yin shahada da sauran abokansa. Su ne masu aiwatar da kisan kai da ayyukan fasadi a duniya. Sun yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran barazana. Abin farin cikin shi ne, dukkanin hukumomin...
    Kotu a kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Ayatullah Baqir Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda Hukumar tsaron kasar Iraki ta sanar a ranar litinin cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aiwatar da zaluncin kisa kan Ayatullahi Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda. Ofishin yada labarai na hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan masu laifin Sa’adoun Sabri da Haitham Abdul Aziz, bayan da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen aiwatar da hukuncin kisa kan Shahadar Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa, Alawiyya Bint al-Huda a...
    Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba. Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya mika sakon gaisuwar idin Nowruz na sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Nowruz, na  shigowar bazara da kuma sabuwar shekara ta Farisa. Putin ya kuma aike da sakon fatan alheri ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar a ranar Juma’a. Nowruz, wanda ke nufin Sabuwar Rana, ita ce ranar farko ta watan Farvardin na kalandar Farisa. Ranar  a mafi yawan lokuta tana kamawa ne a ranar 20 ga Maris amma a duk bayan shekaru tana tana kamawa  daidai da 21 ga Maris. Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ranar Nowruz ta duniya a...
۱