-
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin...
-
Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno. Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sa’annan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta. Mazauna yankin sun bayyana...