2025-12-02@08:03:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1136

«gidauniyar yaki da cutar kansa»:

    Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata,  sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da...
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya...
    Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa. A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar...
    Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri...
    Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta. Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun...
    Sojoji sun yi nasarar cafke wani mutum da ake zargi dan ta’adda ne tare da gano ma’adanar makamai a yayin wani samame da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato. Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama ɗin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alhakin kisan...
    Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da...
    Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk...
    Rahotanni daga kasar ta DRC sun ambaci cewa an ga tsohon shugaban kasar Joseph Kabila a jiya Alhamis a garin Goma wanda yake a karkashin ikon ‘yan tawayen kungiyar M23. Majiyar malaman addinin kirista a yankin ce ta sanar da cewa, ta gayyace shi ne domin ya shiga Tsakani a kawo karshen yakin da ake...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa:...
    A wannan zango na shekaru biyun Tinubu, ma’aikatar yada labarai ta kasa; ita ce ginshikin aiwatar da wadannan dabaru da tsare-tsare, musamman ta fuskar sake fasalin hukumomi, aikewa da sakwannin jan kunne da ladabtarwa da kuma jin ra’ayoyin daidaikun mutane, wanda hakan ya bai wa gwamnatin damar sanin matsalolin ‘yan kasa da kuma hanyoyin da...
    Ambaliyar dai, ta afku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama yana sauka a daren Laraba.   Wani mazaunin garin, Mohammed Usman ya ce tuni aka fara tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwan, amma wasu da dama ba a iya ganin su ba musamman a wuraren da gidaje suka nutse....
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmaci a makon da ya gabata, wanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamnatakewa tsaro da sauransu. Inda muka yi masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su...
    Mutanen da ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja. Mazauna yankin sun kuma ce babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya da ta bi ta yankin ita ma ambaliyar ta yanke ta. Kodayake dai...
    Kasashen kungiyar ‘ the Association of Southeast Asian Nations’ ko ASEAN ta yi allawadai da kisan kiyashiun da ke faruwa a zirin gaza, sannan ta bukaci kasashen duniya su dauki matakan da suka dace don dawo da doka da oda na kasar Falasdinu da aka mamaye, a kuma kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa...
    A wani babban ci gaba na kawo sauyi a tsarin kiwon lafiyar Najeriya, gwamnatin tarayya ta yi  ta kaddamar da ayyuka 16 a asibitin masu tabin hankali na gwamnatin tarayya dake Kware a jihar Sokoto.   Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Ministan Kasa a ma’aikatar Lafiya da walwalar jama’a, Dokta Iziak Salako, ya...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa  ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa;  Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai...
    Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin...
    A cikin wani mataki na ci gaba da sauya fasalin bangarorin noma da kiwo, Gwamnatin Jihar Jigawa na shirin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanonin kiwon kaji na kasar Indiya, wato Srinivasa Farms. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed...
    Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya  masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun...
    Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta buƙaci al’ummar da ke kewayen hanyar Mararaba zuwa Nyanya su kwantar da hankalinsu bayan jin ƙarar wani abu da ya fashe a yammacin ranar Litinin. Lamarin ya faru ne a wata tashar bas da ke kusa da barikin sojoji na Mogadishu a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya. A wata...
    Shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto ya ziyarci kasar Sin daga ran 22 zuwa 26 ga watan Afrilun da ya gabata, bisa gayyatar da takwaransa na Sin Xi Jinping ya yi masa. Yayin ziyararsa, shugabannin biyu sun kai ga matsaya daya kan daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa hulda mai makoma ta bai daya a...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da...
    Baki a Nijeriya da abokansu Sinawa sun nishadantu yayin da suka halarci taron gabatar da fasahar hada shayi ta 2025 da al’adun Yaji, wanda aka yi jiya Asabar a Abuja babban birnin kasar. An gudanar da taron ne a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin da hadin gwiwar cibiyar raya al’adu ta lardin Zhejiang, wadda...
    Ministan gina hanyoyi da ci gaban kasa na JMI Farzaneh Sadegh ta ziyarci kasar Iraki don bin duddugin aikin layin dogo da ake ginawa tsakanin kasashen biyu. Farzaneh Sadegh ta isa bienin Bagdaza a jiya Asabar inda mataimakin ministan sifiri na kasar Iraki da kuma jakadan kasar Iran a Bagdaza suka yi maraba da ita....
    Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta yi kakkausar suka kan kalaman baya-bayan nan da dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Randy Fine ya yi, wanda ya yi kira da a kai wa zirin Gaza hari da makamin Nukiliya. Kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana kalaman dan ‘majalisar a matsayin...
    Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin...
    Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar  Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran...
    “Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wata yarinya ’yar shekara 15 bisa zargin jefa gawar wani jariri a cikin wani banɗaki da ke sansanin ’yan gudun hijira a Monguno. A cewar wata majiyar ’yan sanda a ranar 22 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:15 na safe, an bayar da rahoton cewa, a safiyar...
    Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta zargi shugaban gwamantin kasar Siriya al-Julani da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta bayyana shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani a matsayin azzalumi wanda ya sayar da addininsa tare da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai. Ta yi...
    Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa.   “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza. Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza. Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin...
    “Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar   Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da...
      Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025. Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu...
    An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna. Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood. Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda...
    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni.   Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban...
    Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan...
    Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da...
    Kungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito. Arsenal ta fuskanci matsalolin ‘ƴan wasan gaba a kakar wasan da ke dab da ƙarewa, yayin da ƙungiyar ta gaza lashe kowane irin kofi. Bayan ƙarewa a mataki na biyu a Gasar Premier da samun gurbin...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan...
        Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu. Ban da haka, matsayin musamman na...
    Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu...
    Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan. A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen. Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da...
    Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi...
    Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji. An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji....