2025-11-14@09:19:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 506

«da tsarin jarabawa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
    “Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu. “Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu. “Saboda haka,...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a rundunar arewaci ta rundunar sojin ’yantar da al’ummar Sinawa wato PLA, gabanin Bikin Bazara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji (CMC), a madadin kwamitin kolin da hukumar CMC, ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga dukkan jami’an rundunar soji ta PLA, da sojoji ’yan sanda, da fararen hula dake aiki a rundunar soja, da mambobin kungiyoyin sa kai da ma jam’an tsaro da aka kebe domin bukatar gaggawa. A bana, Bikin Bazara na sabuwar shekarar al’ummar Sinawa ya fado ne a ranar 29 ga watan nan na Janairu. (Fa’iza Mustapha)
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...