2025-09-17@22:17:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 217

«a Arewacin Nijeriya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.   Gwamnan a wajen bikin mika ragamar sansanin da aka samar, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bin sawun ‘yan bindiga har sai an fatattake su da ruguza su da murkushe su.   Dokta Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta’addanci da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.  ...
    Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa. Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga. Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace...
    Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka da suke yankin Djaiba hare-hare a gundumar Ituri a  jiya litinin da dare. Bugu da kari masu dauke da makaman sun kai hari a cikin sansanin ‘yan hijira da suke a cikin wannan yankin kamar yadda shugaban sansanin Antoinnette Nzale ya fadawa manema labaru. Ita dai kungiyar CODECO  gamayya ce ta kungiyoyin da suke dauke da makamai da su ka fito daga kabiluar Landu, manoma....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a yau litinin, a birnin Hamedan. Imam Khumaini (q) ne ya jagoranci kasar zuwa ga nasara a shekara 1979, Juyin juya halin da ya kawo karshen Sarautar Muhammad Reza sha Pahlavi. Ministan ya kara da cewa Jagoran juyin juya halin musulunci ya rika ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Iran kan wannan batun, sannan abinda ya fada shi ne duk wani mai...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
    A zamanin baya, duk da cewa fina-finan nanaye sun fi karbuwa a wajen mutane, amma haka muke kokartawa wajen ganin an shigar da wata koyarwa ta addinin musulinci ko kuma wani abu mai amfani da zai amfanar da al’umma ta wani bangare, amma yanzu duk an daina wannan, masu shirya fina-finai na amfani da labarai masu tsafta da amfanarwa, ba tare da da sanya wakoki ko makamantansu a ciki ba, in ji Malam. “Dalili kuwa shi ne, yanzu ‘ya’yan mutunci da arziki su ne ke yin harkar, sannan kuma su ne suke samun arzikin duniya da na lahira, akwai lokacin da har mata masu zaman kansu din, sai da muka daina samun su idan zamu yi fim, amma yanzu wannan...
    Gwamnatin kasar Argentina ta sanar da ficewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO. Mai magana da yawun shugaban kasar Manuel Adorni ya fadawa taron manema labarai cewa, shugaban kasar Javier Milei, ya umarci ministan harkokin wajen kasar Gerardo Werthein, da ya dauki matakin janye Argentina daga hukumar lafiya ta duniya. Adorni ya ce, ” ‘yan Argentina ba za su kyale wata kungiya ta kasa da kasa ta tsoma baki a harkokin da suka shafi ‘yancin kasarmu ba. “ Ya kara da cewa,”Ya kamata a fayyace cewa Argentina ba ta karbar kudade daga hukumar ta WHO don kula da lafiya, don haka, wannan matakin, kamar yadda wasu ke cewa, a kalla a shafukan sada zumunta, ba ya wakiltar asarar kudade ga kasar,...
    HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan  yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
    Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya ce kasashen turan guda uku wadanda suka hada da Jamus, Faransa da Ingila sun aiko masa da sako inda suke tabbatar haka. A cikin shugaban Muhammad Eslami ya fadawa tashar talabijan ta Presstv irin ci gaban masu yawa wadanda JMI ta samu a cikin shekarun da suka gabata. Shugaban ya kara da cewa sakon da EU3 ya nuna irin yadda rikicin shirin Nukliyar kasar Iran...
    Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a ragar Manchester City bayan da ɗan wasan baya Nathan Ake ya tafka kuskure. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates  Duk da ƙwallon da Haaland ya ci bai hana Arsenal raga raga da City a wasan mako na 24 na gasar Firimiyar  ba, wannan sakamakon ya sanya magoya bayan ƙungiyar sa...
    Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da kasar ke yi na karfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk kasashen da suka nemi tsoma baki a harkar kasarsa. Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama...
    Dandalin sada zumunta na TikTok ya sanar da hada gwiwa da kamfanin tallace-tallace ta kafofin zamani na Aleph Holdings da dandalin sayayya kan intanet na kasar kenya wato Wowzi, wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arziki mai nasaba da kirkire-kirkiren jama’a a kasar Kenya. Carl Jordon, shugaban sashen tallace tallace da harkokin cinikayya a yankin kudu da hamadar Sahara na kamfanin TikTok, ya shaidawa manema labarai a Nairobi cewa, hadin gwiwa da kamfanin Aleph holdings zai saukakawa harkokin kasuwanci a kasar wajen tallata kayayyaki da hidimominsu a kan dandalin wallafa bidiyo na wayar salula. Ya ce hadin gwiwar ya nuna kudurin TikTok na karfafa muhallin kirkire-kirkire na jama’a a cikin gida ta hanyar tabbatar da masu basira sun samu...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara? Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba. Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...