2025-09-17@23:24:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 106
«Ginnery Company»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada. Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na...
Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar Argungu. “Muna godiya da fahimta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da mahalarta wannan biki,” in ji Mataimakin Gwamnan jihar Kebbl Sanata Abubakar Umar Tafida.
Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG ya kai sau biliyan 16.8, wanda ya karu da kashi 18.31 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Bugu da kari, yawan masu kallon shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 ta hanyar talabijin yayin da aka watsa shi kai tsaye a cikin kasar, ya kai kashi 78.88 cikin dari, wanda ya kafa sabon tarihi a cikin...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya fitar da jerin shirye-shiryen shagalin murnar bikin bazara na bana a yau Talata. Shagalin na bana zai kunshi nau’o’in shirye-shirye daban-daban, kamar wake-wake da raye-raye da wasannin kokawa na gargajiya da na siddabaru da sauransu, domin murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta Sin tare da masu kallo dake fadin duniya. A lokaci guda, wasu kafafen yada labarai 2,900 a kasashe da yankuna sama da 200 dake fadin duniya, za su kama tashoshin talabijin na CGTN na kasar Sin na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Rashanci da sauran dandamali dake amfani da harsunan waje har 82, wajen watsawa tare da bayar da rahotannin shagalin bikin bazara na bana....
Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana. “Ya yi kira da a yi la’akari da halin da ake ciki don tabbatar da ci gaba da samar da muhimman ayyukan ci gaba da na jin kai ga al’ummomin da ke da rauni a duniya,” in ji Stephane Dujarric ga manema labarai. ” Ya ce akwai al’umomin da suka dogara da wannan tallafin,” inda ya kara da cewa Amurka na “daya daga cikin manyan masu ba da agaji” a duniya....

An Kammala Gwaje-Gwajen Wasan Kwaikwayo Na Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG Na 2025
An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi. Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)