Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa jihohi 30 da ke kasar nan ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, suna cikin hadarin ambaliyar ruwa, sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a ranar Alhamis da ta gabata, inda fiye da mutum 200 suka rasa rayukansu a Mokwa na Jihar Neja.
Sannan gidajen da dama sun salwanta, wanda ya sa dubban mutane sun rasa muhallinsu, haka kuma mutum 500 sun bace.
- Abubuwan Da Ba A Fada Ba Game Da Mummunar Ambaliyar Ruwan Mokwa
- Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Jihohin da ke fuskantar hadarin ambaliyar ruwa sun hada da Abiya, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Borno, Krus Ribas, Delta, Ebonyi, da Edo.
Sauran sun hada da Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, Zamfara da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli, Injiniya Joseph Utseb, wanda ya bayyana damuwar a wani taron a Abuja, ya kuma ce ambaliyan ruwa a Mokwa ba ta hanyar sakin ruwa daga dam din Kainji da Jebba ba ne, amma sakamakon ruwan sama mai yawa, wanda ya karu sakamakon tasirin canjin yanayi ya haifar da shi.
Ya ce an samu yawan mace-macen ne saboda rashin bin umarnin gargadin ambaliyar ruwa daga mutane a jihar.
Ya bukaci jihohi su dauki matakai don hana mummunar ambaliyar ruwa da ka iya lalata rayuka da kadarori, ministan ya ce, “Ma’aikatar Tarayya ta Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli tana mika ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar Jihar Neja, musamman ga al’ummomin da lamarin ya shafa a Mokwa, wadanda suka fuskanci asara, mutuwa da canjin wuri sakamakon wannan bala’i na ambaliyar ruwa.
“Ina jaddada cewa ambaliyan da aka samu ba ta kasance saboda sakin ruwa daga dam din Kainji ko Jebba ba ne, domin duka dam din suna cikin tsaro.
“Mun yaba da kokarin gaggawa na gwamnatin Jihar Neja da hukumomin yankin, da masu ba da agajin gaggawa da ke aiki ba tare da gajiya ba don bayar da taimako da goyon baya ga wadanda abin ya shafa.
“Ambaliyar ruwan da ta faru a garin Mokwa, ya samo asali ne daga ruwan sama mai yawa sakamakon yanayi mai tsanani, wanda canjin yanayi ya jawo, wani abu da ke tasowa a duniya, wanda ya shafi hanyoyin kwalbatin na yankin.
“Bugu da kari, gine-gine marasa tsari sun toshe hanyoyin ruwa na Kogin Dingi, wanda ya tunbaza har ya yi ambaliya sakamakon ruwan saka kamar da bakin kwarya. Rashin hanyoyin madatsun ruwa sun kara yin tasirin ambaliyar ruwan a garin.
“‘Yan Nijeriya za su iya tuna cewa Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya, ta hanyar Hukumar Kula da Madatsun Ruwa ta Nijeriya (NIHSA), a cikin hasashen ambaliyar ruwa na 2025, a ranar 10 ga Afrilu, 2025, ta yi hasashen ambaliyar ruwa a cikin kananan hukumomi 19 na Jihar Neja, ciki har da karamar hukumar Mokwa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp